logo

HAUSA

Jakadan Sin: Abin kunya ne ga Amurka ta lissafa yunkurin lalata tasirin kasar Sin a matsayin nasara a gaban MDD

2022-01-23 16:50:19 CRI

Jakadan Sin: Abin kunya ne ga Amurka ta lissafa yunkurin lalata tasirin kasar Sin a matsayin nasara a gaban MDD_fororder_780438397de9446ab533b00082fd9e10

A tsokacin da ya gabatar game da takardar bayanan da ofishin jakadancin Amurka ya gabatarwa MDD, jakadan kasar Sin ya bayyana a ranar Juma’a cewa, abin dariya yadda ofishin jakadancin Amurka ya bayyana yunkurin lalata tasirin kasar Sin a matsayin nasarar da ta cimma har ma ta fito gaban hukumar ta kasa da kasa tana wannan ikirarin.

A ranar Alhamis, ofishin jakadancin kasar Amurka ya wallafa a shafinsa na intanet wata takardar bayanai a gaban MDD mai taken “Maido da shugabancin Amurka a MDD a matsayin nasarar da shugaba Biden ya cimma cikin shekara guda," inda aka gabatar da zarge-zarge masara tushe kan kasar Sin.

A martanin da ya mayar kan tambayoyin da ‘yan jarida suka yi masa, Zhang Jun, wakilin dindindin na kasar Sin a MDD, ya bayyana irin rashin hikimomin dake kumshe cikin takardar bayanan da ofishin jakadancin Amurka ya gabatar, inda ya bayyana cewa, abin kunya ne kuma lamarin ya wuce hankali a ce Amurka tana lissafa neman dakile tasirin kasar Sin a gaban MDD a matsayin wani muhimmin aiki kuma a matsayin babbar nasarar da ta cimma.

Zhang ya ce, gudunmawar da kasar Sin ta bayar ga zaman lafiya da cigaban duniya, da irin goyon bayan da take baiwa MDD da kuma taimakon da take baiwa sauran kasashen duniya suna da matukar muhimmanci kuma kowa yana kallon yadda lamarin yake faruwa. Abinda kasar Sin take bukata shine yin hadin gwiwar moriyar juna maimakon yin baba-kere, da tabbatar da daidaito maimakon yin zalunci, da gudanar da  al’amurra a bayyane gami da shigar da kowane bangare maimakon kafa shinge da shamaki, da kuma tabbatar da zaman lafiya maimakon neman tada husuma da yin fito-na-fito.

Game da yadda Amurka take kokarin bata sunan kasar Sin ta hanyar fakewa da batun yanayin hakkin dan adam a yankin Xinjiang, Zhang ya ce, “Gaskiyar magana shi ne, yankin Xinjiang yana cin moriyar zaman lafiya, da samun bunkasuwa. Rayuwar Sinawa tana kara kyautata a kullum."

Zhang ya kara da cewa, Amurka, maimakon ta mayar da hankali kan neman daga matsayin hadin gwiwar kasa da kasa, sai ta mayar da hankali kan batun wani irin tunani na neman yin fito-na-fito da neman lalata tasirin kasar Sin da sauran kasashe, wanda yin hakan babbar matsala ce dake haifar da koma baya ga hadin kai da amincewa da juna a tsakanin mambobin kasashe, kana yana haifar da tarnaki ga MDD wajen sauke nauyin dake bisa wuyanta.(Ahmad)