logo

HAUSA

Ana zargin al-Shabab da kone wasu manyan motoci 8 a gabar ruwan Kenya

2022-01-24 11:41:53 CRI

Ana zargin al-Shabab da kone wasu manyan motoci 8 a gabar ruwan Kenya_fororder_220124-saminu-Kenya.jpg

A kalla manyan motoci 8 dauke da kayayyakin gini ne suka kone kurmus, lokacin da wasu mahara da ake zaton mayakan Al-shabab ne suka cinna musu wuta a jiya Lahadi, a garin Hindi mai nisan kilomita 29 daga gundumar Lamu ta kasar Kenya.

Kwamishinan gundumar Lamu dake bakin tekun Kenya Mr. Irungu Macharia ya ce, motocin mallakin kamfanin gine gine na kasar Sin CCCC ne, wanda ke gina babbar hanyar mota da za ta hade gabar teku dake Lamu zuwa Sudan ta kudu da Habasha, ko LAPSSET a takaice.

Mr. Macharia ya ce ba a samu asarar rayuka yayin gobarar ba, sai dai karancin hidimar layukan waya a yankin ta kawo tsaiko, wajen kiran ’yan sanda a kan lokaci, amma duk da haka a cewarsa, jami’an tsaro sun bazama domin zakulo wadanda suka aikata wannan ta’asa, an kuma tsaurara matakan tsaro a yankin da lamarin ya auku.    (Saminu)