logo

HAUSA

Kudurin kasar Sin na fadada bude kofa ga kasashen waje ba zai canja ba

2022-01-24 20:49:13 cri

Kudurin kasar Sin na fadada bude kofa ga kasashen waje ba zai canja ba_fororder_src=http___5b0988e595225.cdn.sohucs.com_q_70,c_zoom,w_640_images_20181219_68ee78cce7e54c4c912ccbca4ba3bcb7.jpeg&refer=http___5b0988e595225.cdn.sohucs

Dangane da yadda rahotannin hukumomin ketare suka karrama yanayin kasuwancin kasar Sin, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian ya jaddada a gun taron manema labaru da aka saba shiryawa a yau Litinin cewa, kudurin kasar Sin na kara fadada bude kofa ga kasashen waje ba zai canja ba. Kuma niyyarta ta raba damar ci gaba da duniya ita ma ba za ta canja ba, kudirin inganta tattalin arzikin duniya zuwa mai salon bude kofa, da daidaito, da samun nasara tare ba zai canza ba.

Rahotanni sun bayyana cewa, kwanan baya kungiyar ‘yan kasuwar kasar Jamus dake kasar Sin da kamfanin harkokin kudi na KPMG, sun fitar da wani sakamakon bincike game da amincewa da harkokin kasuwanci na shekarar 2021/2022 tare, wanda ya nuna cewa, har yanzu kamfanonin Jamus dake kasar Sin, suna cike da kwarin gwiwa kan ci gaban kasuwannin kasar Sin, kuma kusan kashi 60% na kamfanonin Jamus dake kasar Sin, sun samu bunkasuwar kasuwanci a shekarar 2021. Bugu da kari, kungiyar ‘yan kasuwar Amurka dake Hong Kong, ta fitar da "Rahoton binciken amincewar kasuwanci na 2022", inda aka nuna cewa, karin kamfanonin Amurka dake Hong Kong, sun kara nuna kwarin gwiwa kan yanayin kasuwancin Hong Kong. (Bilkisu Xin)