logo

HAUSA

Shugaban kasar Malawi ya rusa majalisar ministocinsa

2022-01-25 09:52:21 CRI

Shugaban kasar Malawi ya rusa majalisar ministocinsa_fororder_0125-Malawi-Ahmad

Shugaban kasar Malawi Lazarus Chakwera, a ranar Litinin ya rusa majalisar zartaswar kasar yayin da ake yada jita-jitar cewa manyan masu rike da mukaman siyasar kasar, da ma’aikatan hukumar shari’a da sauran jami’ai ana zarginsu da hannu wajen ayyukan rashawa wanda ke da alaka da hamshakin dan kasuwar kasar ta Malawi mazauni kasar Birtaniya, Zuneth Sattar, wanda duka hukumomin yaki da rashawa na Malawi da Birtaniya suke binciken shi.

Wannan batu ya biyo bayan wata hira ta wayar tarho da ta bulla wadda ta gudana tsakanin babbar jami’ar hukumar yaki da rashawa ta Malawi (ACB) Martha Chizuma, da wani wanda ya kira wayar wanda ba a tantance ba, inda shugabar hukumar ta ACB ta bayyana wasu bayanai masu muhimmanci dake shafar bincike kan zargin ayyukan rashawa.

Shugaban kasar ya aike da sakon gargadi ga Chizuma bisa ga fitar da kalaman tattaunawar da ta gudanar ta wayar, inda ya bayyana lamarin da cewa rashin da’a ne. (Ahmad)