in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kara cin danyun 'ya'yan itatuwa yana iya rage barazanar kamuwa da ciwon zuciya da shan inna
2017-08-21 14:03:16 cri

Turawa kan cewa, cin tuffa a ko wace rana, na kau da bukatar ganin likita. Masu nazari daga kasashen Birtaniya da Sin sun gudanar da wani nazari, inda suka nuna cewa, kara cin danyun 'ya'yan itatuwa yana iya rage barazanar kamuwa da ciwon zuciya da shan inna.

Masu nazari daga jami'ar Oxford da kwalejin nazarin kimiyyar likitanci na kasar Sin sun gudanar da nazarin cikin hadin gwiwa. Sakamakon nazarinsu ya shaida cewa, in an kwatanta wadanda ba safai su kan ci 'ya'yan itatuwa ba, barazanar kamuwa da ciwon zuciya da shan inna da wadanda su kan ci danyun 'ya'yan itatuwa, kamar tuffa, lemu, fiya, suke fuskanta ta ragu sosai.

Masu nazarin sun gudanar da nazarinsu kan mutane kimanin dubu 500 daga wurare guda 10 na kasar Sin, domin yin hasashen kamuwa da cututtukan dake addabar mutum sannu a hankali a nan gaba. Masu nazarin sun tattara bayanan da ke shafar lafiyar mutane, ciki had da al'adar cin abinci, da kuma cututtukan da suke kamuwa da su da kuma mutuwarsu cikin shekaru 7.

Sakamakon bayanan sun shaida cewa, cin danyun 'ya'yan itatuwa giram 100 a ko wace rana, yana iya rage sulusin barazanar mutuwa sakamakon cututtukan da suka shafi zuciya da jijiya.

Masu nazarin sun yi nuni da cewa, watakila dalilin da ya sa hakan shi ne domin 'ya'yan itatuwa cike suke da sinadarin Potassium, sinadarin dake taimaka ga narkas da abinci a jikin mutum, da dai sauransu. Amma wasu babu, ko kuma akwai sinadarin Sodium, da kiba, da Calories kadan ne a cikinsu. Ban da haka kuma, mutanen Sin ba su cin isassun 'ya'yan itatuwa, idan an kwatanta da mutanen kasashen Turai da Amurka, don haka ga alama, kara cin danyun 'ya'yan itatuwa ya fi amfani ga lafiyar mutanen Sin.

Amma duk da haka, masu nazarin sun jaddada cewa, ba a kai ga tabbatar da alakar da ke tsakanin cin 'ya'yan itatuwa, da kuma raguwar barazanar kamuwa da cututtukan da suka shafi zuciya da jijiya ba tukunan. Idan an tabbatar da irin wannan alaka, kana kuma, ko wane Basinne ya rika cin isassun danyun 'ya'yan itatuwa a ko wace rana, to, yawan wadanda suke mutuwa sakamakon cututtukan da suka shafi zuciya da jijiya zai ragu fiye da mutum dubu 500 a ko wace shekara, ciki had da wasu dubu 200 da suka mutu kafin shekarunsu suka kai 70 da haihuwa. Har ila yau za a iya kiyaye karin mutane daga kamuwa da ciwon zuciya da kuma shan inna. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China