in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yawan yara da matasa masu kiba ya ninka sau 10 cikin shekaru 40 da suka wuce
2018-06-11 06:37:32 cri

Ranar 11 ga watan Oktoba, rana ce ta matsalar kiba ta duniya, wadda kawancen kula da matsalar kiba na kasa da kasa ya tsai da. Hukumar kiwon lafiya ta kasa da kasa wato WHO da sauran hukumomi sun kaddamar da rahotonsu da cewa, a cikin shekaru 40 da suka wuce, yawan kananan yara da matasa masu kiba a duniyarmu baki daya ya ninka sau 10, lamarin da ya zama rikicin lafiya ta kasa da kasa.

Rahoton ya tantance bayanan da suka shafi nauyin jikin mutane kusan miliyan 130 wadanda shekarunsu suka wuce 5 a duniya da kuma tsayin jikinsu, ciki had da wadanda shekarunsu suka wuce 5, amma ba su kai 19 a duniya ba miliyan 31.5, da kuma wadanda shekarunsu suka wuce 20 a duniya miliyan 97.4, lamarin da ya nuna mana sauye-sauyen nauyin jikin kananan yara da matasa da tsayinsu da kuma yadda suke fama da matsalar kiba daga shekarar 1975 zuwa 2016 a duk duniya. Nazarin da aka gudanar ya fi shafar yawan mutane ya zuwa yanzu.

Adadin ya shaida mana cewa, a cikin shekaru 40 da suka gabata, yawan masu kiba wadanda shekarunsu suka wuce 5, amma ba su kai 19 a duniya ba ya ninka sau 10 ko fiye da haka, adadin da ya kai miliyan 124 a shekarar 2016. Rahoton ya kuma kiyasta cewa, idan haka lamarin zai ci gaba, to ya zuwa shekarar 2022, yawan kananan yara da matasa masu kiba a duk duniya zai fi na sirara.

Masu nazarin sun yi bayanin cewa, wadannan sauye-sauye sun ta da hankalin mutane sosai, wadanda kuma suka bayyana illar da matakan sayar da abinci da kuma manufofin abinci suka haddasa a duniya.

Har ila yau, sun nuna cewa, abinci masu gina jiki sun yi tsada sosai ga iyalai masu fama da talauci, don haka wajibi ne a kara ba su taimako, kana a kara bai wa kananan yara da matasa masu fama da talauci abinci masu gina jiki. Sa'an nan kuma, hukumomi masu ruwa da tsaki su kafa dokoki da dora haraji kan wasu kayayyaki domin kiyaye kananan yara daga abinci marasa gina jiki, suna cewa, idan ba haka ba, wadannan kananan yara da matasa masu kiba za su fuskanci babbar barazanar kamuwa da ciwon sukari da dai sauransu a nan gaba.

A sa'i daya kuma, hukumar WHO ta kaddamar da wani shirin hana kanana yara yin kiba domin daidaita batutuwa masu ruwa da tsaki, a kokarin bai wa gwamnatocin kasa da kasa jagora. Matakan da aka tanada cikin shirin sun hada da sa kaimi kan kara cin abinci masu gina jiki da motsa jiki, kara mai da hankali kan kiwon lafiyar mata kafin samun ciki da kuma lokacin samun ciki, bai wa kananan yara jagora kan cin abinci da motsa jiki, inganta ayyukan kula da yadda kananan yara da matasa suke ci abinci masu gina jiki da dai sauransu. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China