in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tarihin fama da matsalar tunani yana da nasaba da barazanar mutuwa sakamakon cutar sankara
2019-06-11 13:52:25 cri


Mujallar cutar kansa ta kasar Birtaniya ta kaddamar da wani sabon nazari da cewa, idan masu fama da cutar sankara sun taba kamuwa da lalurar tunani a baya, su kan fuskanci karin barazanar mutuwa. Don haka masana sun ba da shawarar cewa, yayin da likitoci suke ba da jinya ga masu fama da cutar sankara, kamata ya yi su lura da ko sun taba gamuwa da lalurar tunani a baya. Sa'an nan kuma wadanda suka taba kamuwa da matsalar tunani, ya dace su mai da hankali kan yin rigakafin kamuwa da cutar sankara.

Masu nazari daga kasar Canada sun gudanar da nazarinsu kan 'yan kasar Canada masu fama da cutar sankara dubu 676, sun kuma tantance yadda suka je ganin likitoci da suka kware a fannin lalurar tunani shekaru 5 kafin a tabbatar ko sun kamu da cutar sankara. Sakamakon binciken ya nuna cewa, kara zuwa ganin wadannan likitoci, ya sa barazanar da ake fuskanta sakamakon kamuwa da cutar sankara tana kara karuwa.

Alal misali, gwargwadon masu fama da cutar sankara da ba su kamu da lalurar tunani ba a baya, barazanar mutuwa da masu fama da cutar sankara da suka taba fama da ciwon tunani suke fuskanta ta karu da kaso 5. Idan sun taba zuwa asibiti neman maganin matsalar tunanin da suke fama da ita, barazanar za ta karu da kaso 73, musamman ma wadanda suka yi fama da cutar sankarar mafitsara da kuma hanji.

Masu nazarin sun yi bayani da cewa, sakamakon nazarinsu ya shaida cewa, watakila yadda masu fama da cutar sankara suke cikin koshin lafiya ta fuskar tunani, tana taimakawa wajen tsawaita rayuwarsu. Mai yiwuwa ne bakin cikin da ke ransu da kuma babbar matsin lamba za su iya hana tsarin kariyar jiki ya gano tare da kai hari kan kwayoyin halittun dake haddasa cutar sankara. Saboda haka yayin da likitoci suke ba da jinya ga masu fama da cutar sankara, kamata ya yi su kula da ko sun taba gamuwa da matsalar tunani a baya.

Amma duk da haka, masu nazarin sun kara da cewa, sakamakon nazarinsu ya shaida cewa, barazanar mutuwa da masu fama da cutar sankara da suka taba magance matsalar ciwon tunani suke fuskanta ta fi yawa. Amma babu wata shaida da ke nuna cewa, akwai wata alakar kai tsaye a tsakaninsu. Don haka akwai bukatar ci gaba da nazari a wannan fanni.

Ban da haka kuma, wasu masu nazari na daban suna ganin cewa, wannan nazari ya kuma nuna cewa, kamata ya yi masu fama da matsalar tunani su rika binciken lafiyarsu ta fuskar kamuwa da cutar sankara daga lokaci zuwa lokaci. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China