in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
WHO ta musunta jita-jita da aka yi kan allurar rigakafin kamuwa da ciwo (2)
2019-10-08 07:01:18 cri

Sakamakon shekaru 70 da kasar Sin ta dauka wajen raya kasa a fannoni daban daban, ya sa ya zuwa yanzu yawan mutanen da aka yi musu allurar rigakafin kamuwa da cututtuka ya wuce kaso 90 bisa jimillar yawan mutanen kasar. Allurar rigakafin na kare mutanen Sin yadda ya kamata, amma akwai wasu jita-jita dangane da allurar rigakafin, don haka kwanan baya, hukumar kiwon lafiya ta kasa da kasa wato WHO ta kaddamar da wani bayanin ilmantar da jama'a cikin Sinanci da Turanci da wasu harsuna a kan shafinta na yanar gizo ta Internet, inda ta musunta jita-jita da dama dangane da yin allurar rigakafin kamuwa da cututtuka.

Wasu kan ce, sakamakon yin allurar rigakafin kamuwa da cututtuka ya sa babu rahotannin bullowar wasu cututtuka a kasarsu, don haka ba su bukatar a yi musu allurar rigakafin. A'a, ba haka ba ne! Hukumar WHO ta ce, ko da yake yanzu ba a samun barkewar wasu cututtuka a wasu kasashe, amma kwayoyin cututtukan suna yaduwa a wasu sassan duniya. Alal misali, a yammacin nahiyar Turai, tun daga shekarar 2005 har zuwa yanzu, cutar kyanda tana yaduwa tsakanin mutanen da ba a yi musu allura ba a kasashen Austria, Denmark, Belguim, Faransa, Jamus, Italiya, Spain, Switzerland da Birtaniya. Kamata ya yi ko wane mutum ya ba da gudummowa wajen tabbatar da lafiyar al'umma ta hanyar yin allurar rigakafin kamuwa da cututtuka.

Wasu na ganin cewa, wasu kananan yara suna kamu da wasu cututtuka, kuma ana tausaya musu, amma da kyar a kare su daga kamuwa da cututtukan. A'a, ba haka ba ne! Hukumar WHO ta ce, ana iya kare kananan yara daga kamuwa da wasu munanan cututtuka, kamar kyanda, hangu, bakon dauron da dai irinsu, wadanda su kan haifar da cututtuka na daban tsakanin kananan yara da baligai. Ana iya kaucewa kamuwa da cututtukan ne ta hanyar yin allura. Idan ba a yi wa kananan yara allura ba, su kan kamu da cututtuka cikin sauki.

Idan an yi wa kananan yara allurar rigakafin kamuwa da cututtuka iri-iri 2 ko fiye da haka a lokaci guda, za su kara fuskantar barazanar samun mummunar illa, haka kuma tsarin sassan jikinsu na kin kamuwa da cuta zai kara fuskantar matsin lamba fiye da yadda yake iya daidaitawa. A'a, ba haka ba ne! Hukumar WHO ta ce, abubuwan shaida sun nuna cewa, yi wa kananan yara allurar rigakafin kamuwa da cututtuka iri-iri guda 2 ko fiye da haka a lokaci guda ba zai kawo illa ga tsarin sassan jikinsu na kin kamuwa da cuta ba, kuma bisa yin hakan, za a yi tsimin lokaci da kuma kudi da yawa. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China