Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sabon sauyin da ya faru a birnin Shiyan na lardin Hubei na kasar Sin
2019-05-27 08:22:31        cri



A babban dam na Danjiangkou mai tsayin mita 176.6, an ga ruwa yana zuba daga sama cikin sauri, inda ake samar da wutar lantarki da karfin ruwa, akan dam din kuwa, an ga ruwan tafki mai tsabta, inda ake kiran shi madatsar ruwan Dan jiangkou, birnin Shiyan yana sauka ne a kusa da wurin.

A cikin dakin kera motoci na kamfanin kera manyan motocin daukar kayayyaki na Dongfeng dake birnin Shiyan, Yang Guohua, wadda ita ce fitaciyar ma'aikatar kasar Sin ta yi mana bayani kan babban sauyen da ya faru a kamfanin a cikin 'yan shekarun da suka gabata, inda ta bayyana cewa, "A baya adadin na'urorin wutar lantarkin da ake amfani dasu yayin kera motoci bai kai kaso goma bisa dari ba, wato bai wuci kaso biyar zuwa takwas bisa dari kawai ba, amma yanzu ya riga ya kai sama da talatin bisa dari."

An samu asalin sansanin kera manyan motocin daukar kayayyaki na kamfanin Dongfeng ne a birnin Shiyan, a halin yanzu, aikin kera manyan motocin daukar kayayyaki na birnin ya riga ya kai sahun gaba a fadin kasar Sin, har ma a fadin duniya, wato ya kai matsayin koli a kasar Sin, haka kuma ya kai matsayi na uku a fadin duniya, ana iya cewa, birnin Shiyan ya kasance cibiyar kera manyan motocin daukar kayayyaki mafi girma a kasar Sin, kawo yanzu adadin kamfanonin kera motoci a birnin ya kai sama da 600, adadin ma'aikatan dake aiki a cikin kamfanonin ya zarta dubu 200. Ban da babban kamfanin kera motoci na Dongfeng, an kuma kafa kamfanoni matsakaita da kanana ta hanyar yin kirkire-kirkire da dama a birnin.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China