Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An shirya taron cigaban "ziri daya da hanya daya" da hanyar siliki ta kan teku a Chongqing
2019-06-04 09:35:14        cri

Birnin Chongqing dake shiyyar kudu maso yammacin kasar Sin ya karbi bakuncin taron dandalin bunkasa cigaban "ziri daya da hanya daya" da hanyar siliki da kuma hanyar kan teku.

Taron dandalin na "ziri daya da hanya daya" bisa hadin gwiwar raya hanyar kan tudu da kan teku kungiyar kwararrun masanan hanyar siliki da gwamnatin mulkin birnin Chongqing ne suka dauki nauyin taron tsakanin ranakun 2-4 ga watan Yuni.

Mahalarta taron sun cimma matsaya game da raya cigaban hanyar kan tudu da teku karkashin shawarar "ziri daya da hanya daya" bisa shawarar da hukumar mulkin Chongqing ta amince da ita.

Shawarar ta bukaci dukkan bangarorin da abin ya shafa da su yi kyakkyawan amfani da tsarin sufuri na kan teku da hanyar teku, wajen yin hadin gwiwa don raya tattalin arzikin kan tudu da na cikin teku, sannan kasa da kasa su kara yin hadin gwiwa wajen bunkasa harkokin masana'antu, da kara darajar kayayyakin da masana'antun ke sarrafawa.

Taron ya kuma bukaci bunkasa ci gaban tattalin arziki, da yin hadin gwiwa don raya ci gaba da yin musayar nasarori, domin bunkasa ci gaban kasa da kasa cikin lumana bisa hadin gwiwa.

Chen Min'er, mamban hukumar siyasa na kwamitin tsakiyar jamiyyar kwaminis ta kasar Sin CPC kana sakataren CPC na hukumar mulkin birnin Chongqing ya bayyana cewa, "Chongqing yana da wani muhimmin matsayi da tasiri ta fuskar hada yankuna daban daban wanda ya shafi rawar da yake takawa ga raya ci gaban hanyar kan tudu da kan teku karkashin shawarar 'ziri daya da hanya daya'," (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China