Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
'Ya mace ta kasar Rasha Tania da malaminta na kasar Sin Li Yugang
2019-06-11 09:40:21        cri

Kafin zuwan shekarar 2019. Gidan Radio Metro na birnin Saint Petersburg dake kasar Rasha ya watsa wata wakar kasar Sin ce mai taken "Saduwa da kai". Yayin da Tania, 'ya mace ta kasar Rasha dake zauna a dakin daukar murya ke sauraron wakar, ta yi kuka, ganin yadda ta riga ta bar garinta na biyu wato kasar Sin har na tsawon rabin shekara.

Tania, wata daliba ce dake karatu a kwalejin oriental ta Jami'ar nazarin ilmin tattalin arziki ta kasar Rasha. A shekarar 2017, ta zo kasar Sin don karo ilminta kan harshen Sinanci a Jami'ar Shenyang. A wani karo, Tania ta ji wakar "Saduwa da kai" da mawaki Li Yugang ya rera.

"A wancan lokaci, ina ganin cewa, lallai na gano wani abu mai daraja sosai", Yayin da Tania ta tuna yadda take ji yayin da ta saurari wannan wakar, ta ce, "Ko da ni wata bakuwa ce, amma muryarsa ta burge ni kwarai, wadda ke nuna al'adun kasar Sin sosai."

Tun bayan karon farkon da Tania ta saurari wakar da Li Yugang ya rera, ta fara sha'awar wakokinsa. Amma a hakika dai, Tania bata daukar kanta a matsayin wata mai sha'awar mawaki tauraro, a maimakon haka ta maida kanta a matsayin dalibar Li Yugang, wato ta fara yin nazari akan dangantakar dake tsakanin wakokin Li Yugang da al'adun kasar Sin. Banda fassara wakokin zuwa harshen Rashanci, ta kuma yi nazari kan ilmin tarihi da al'adun Sin da wakokin suka shafa.

"Ina daukar Li Yugang a matsayin malamina, bayan da na fassara wakokin da ya rera, ilmina kan al'adun Sin ya karu sosai. Ina da aniyar yada wakokinta ga al'ummar Rasha domin Rashawa su kara fahimtar al'adun Sin."

A watan Yuni na shekarar 2018, an nuna wasan kwaikwayon wake-wake da raye-raye mai taken "Kahon samun basira" a birnin Shenyang, wanda Li Yugang yasa hannu a ciki. Da jin labarin, Tania dake karatu a Shenyang ta yi matukar fara'a, kuma ta tsaida kudurin rubutawa malaminta wata wasika.

"gaskiya dai wannan wata doguwar wasika ce. Da farko dai na yi rubutu da harshen Rashanci, sa'an nan na fassarata zuwa Sinanci, kuma na bukaci malamina Basinne da ya duba da kuma gyara wasikar."

A cikin wannan wasikar, Tania ta rubuta cewa, "Sannunka, Malam Li Yugang. Ina so in gaya maka, kwarewarka wajen fasaha ta kara kwarin gwiwata, kuma ta burge ni, har ma ta fadakar da ni sosai, Don haka ina zaton cewa, tabbas ne zan gabatarwa Rashawa fasaharka. Saboda kai ne, na gano karin kyawawan al'adun al'ummar Sin. Domin kara fahimtata, na saurari wakokinka sau da yawa, kuma na kalli intabiyu da aka yi maka sau da yawa, bayan da na samu sabbin labarai, kullum na roki malamina domin samun karin bayani a shafin Intanet. Gaskiya dai ka shigar da ni wata kyakkyawar duniya, kai babban malamina ne."

Bayan da ta gama rubutawa, Tania ta fara damuwa, wato ko ta yaya zata ba Li Yugang wasikar?

Labarin Tania ya burge abokanta sosai, don haka sun tsaida kudurin bata wani abin mamaki.

"A wancan lokaci, ina tsara wani bidiyo kan labaran dalibai 'yan kasashen waje dake karatu a Sin. Tania ita ce mafi muhimmnanci a cikin bidiyon. Wata daliba ce ita, amma ta gudanar da dimbin ayyuka kan yada al'adun Sin."

Li Honglei, babban daraktan na bidiyo mai taken "karo ilmi a Lardin Liaoning" kuma shugaban sashen rediyo da talibijin na jami'ar Shenyang ya bayyana hakan. Bisa kokarin da Li Honglei ya yi, a karshe dai Li Yugang ya samu wasikar Tania. Da ya san cewa, akwai wata 'yar Rasha da take sha'awar wakokinsa, kuma ta gabatar dasu ga masu sauraro na ketare, lallai ya ji mamaki kwarai da gaske. Li Yugang ya ce,

"Mai ba ni taimako ya gaya mini cewa, wata 'yar Rasha na sha'awar wakokina sosai, har ma ta maida su a matsayin karfinta na koyon al'adun Sin. Da jin labarin, lallai na yi shakku a kansa. Amma bayan da na ga bayaninta kan abubuwan da ta yi, lallai ta burge ni sosai."

Sabo da haka, a ranar 10 ga watan Yuni, kafin a fara nuna wasan kwaikwayo na "Kahon samun basira" a birnin Shenyang, Li Honglei ya kai Tania dakin shirye-shirye na wurin nuna wasan kwaikwayon. Amma wannan ganawar bazata ta sa Tania bata san yadda za ta yi ba, har ma tana son gudu. Tania ta ce,

"Da na isa wajen kofar dakin kwalliya na Malam Li Yugang, lallai ina jin tsoro. Za a nuna wasan kwaikwayon bada jimawa ba, bana son kawo masa matsala, wadda zai sa na ji kunya sosai."

A daidai wannan lokaci, kofar dakin kwaliya ta bude kwatsam, ba Li Yugang bane da ya fito, lamarin da ya sa hankalin Tania ya kwanta, amma a sa'i daya kuma ta yi dan bacin rai kadan. Mai bada taimako na Li Yugang ya gayyaci Tania ta shiga dakin, sa'an na ya yi hira tare da ita. A lokacin kuma, kofar dakin ta sake budewa, ashe Li Yugang ne. Da ganin surarsa a gaban idanunta, Tania ta rasa abin da ya kamata ta yi.

"Ya bani wata alawa mai tsinke, amma ni ban fadi kome ba, ban san yadda zan fada ba."

"Ban san dalilin da yasa na burge ta ba, amma ina zaton, babu shakka saboda al'adun Sin ne. Lallai ta gudanar da wani babban aiki abun alfahari, ganin yadda take kokarin yada al'adun kasar Sin a kasar ta wato Rasha wadda ke da dogon tarihi."

Tania ta koma birnin St. Petersburg na kasar Rasha bayan da ta kammala karatun karo ilmi na gajeren lokaci. Sa'an nan ta kafa wani dandali na 'yan Rasha masu sha'awar Li Yugang a shafin intanet mafi karbuwa a kasar, domin fassara da yada wakoki da labari na Li Yugang. Tania tana ganin cewa, game da 'yan Rasha, babu wuyar fahimtar wakokin Li Yugang. A maimakon haka, ta kalmomin wakokin, 'yan Rasha zasu iya fahimtar ma'anarsu daga zuciya.

"Alal misali, ga waka mai taken 'garina' da ya tsara da kansa, da na saurari wakar a karon farko, na tuna da shahararren mawaki na Rasha Sergei Esenin. Ina da imanin cewa, idan Rashawa suka saurari wakar, zasu ji dadi sosai, sakamakon samun abin da suke sabawa dashi."

Game da makomarta a nan gaba, Tania ta ce tana da dimbin shirye-shirye, wadanda dukkansu nada alaka da batun yada al'adun Sinawa. Tana da shirin kafa wata makarantar koyar da Sinanci a birnin St. Petersburg. Ta ce, "Na san cewa, zan haye wahalhalu domin cimma burina. Yadda Li Yugang ke yi ya kara mini kwarin gwiwa sosai."

Ban da ita, malaminta Li Yugang wanda ke zauna a birnin Beijing ke kokarin yada al'adun Sin zuwa ketare.

"Tun bayan da na fara sa hannu cikin wasan kwaikwayo na wake-wake, da raye-raye mai taken 'Shucin gizo', na san cewa, akwai wani nauyin da ke wuyana, wato yada al'adun gargajiyar Sin. Gaskiya dai ina so nuna wasu abubuwan fasaha masu ma'ana sosai."

A watan Afrilun shekarar 2019, Li Yugang ya nuna wasan kwaikwayo mai taken "Labarin Madam Wang Zhaojun" a birnin Beijing, wanda zai nuna shi a duk duniya. Wannan wasan kwaikwayo ma ya kwashe shekaru shida da Li Yugang da kungiyarsa suka tsara shi, wanda ya bayyana tunanin samun jituwa dake cikin al'adun Sinawa. Li yana fatan za a nuna wasan kwaikwayon a birnin St. Petersburg wata rana domin Rashawa masu sha'awar al'adun Sin kamar Tania zasu iya kallonsa.

Wannan shi ma ya kasance buri ne na Tania. A cikin wasikar da ta rubutawa malaminsa Li Yugang, ta ce, "Kullum ina tunanin yadda kake tsayawa akan dakalin dakin nuna wasannin kwaikwayo na Malinsky. Lallai wannan abune da ya cancance ka sosai. Ya kamata ka samu karbuwa da tafuka daga wajenmu. Don haka ina so in baka taimako, kuma na riga na shirya sosai. Na san mene ne burinka, kuma ina so in taimaka maka wajen cimmawa."(Kande Gao)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China