Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
WHOˇGBarkewar annobar Ebola a Kongo bai kasance barazanar lafiyar kasa da kasa ba
2019-06-15 16:11:56        cri
Hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta bayyana matukar damuwa game da halin da ake ciki na barkewar annobar cutar Ebola a jamhuriyar demokaradiyyar Kongo (DRC), sai dai duk da haka hukumar ta ce yanayin da ake ciki bai kai matakin barazanar lafiya na kasa da kasa ba.

Darakta janar na hukumar ta WHO Dr. Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya kira wani muhimmin taro a ranar Juma'a domin tattauna batun dokokin kwamitin hukumar lafiyar ta kasa da kasa domin daukar matakan gaggawa kan barkewar cutar Ebolar a DRC, inda aka yanke hukuncin cewa, yanayin cutar bai cika dukkan sharrudan da suka mayar da cutar matakin lafiya na gaggawa na kasa da kasa ba.

Wannan shi ne karo na 3 da kwamitin ke tattaunawa game da barkewar cutar, bayan taruka biyu da aka gudanar a tsakiyar watan Afrilu da Oktoban shekarar da ta gabata.

Kwamitin ya bayyana matukar damuwa game da yanayin da ake ciki na barkewar annobar Ebolar, duk da irin nasarorin da aka samu na karancin yiwuwar bazuwar cutar, amma binciken ya nuna cewa, yanayin bazuwar cutar a yankuna kamar su Mabalako ya kasance babbar barazana ga al'ummomin yankin da ma harkokin tsaron yankin. Bugu da kari, matakan da ake dauka yana ci gaba da fuskantar barazana sakamakon karancin kudaden gudanarwa da karancin jami'an gudanar da shirin. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China