Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mambobin CPPCC sun ba da shawara kan yadda za a raya kamfanoni masu zaman kansu
2019-06-24 14:41:39        cri


Yau za mu yi muku bayani kan shawarwarin da mambobin majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin wato CPPCC a takaice suka gabatar kan yadda za a samu ci gaban kamfanoni masu zaman kansu mai inganci a kasar, da matakan da gwamnatin kasar take dauka domin cimma wannan burin.

A ranar 6 ga watan Maris na bana a nan birnin Beijing, an kira taron ganawa da manema labarai na taro na biyu na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin karo na 13, inda wasu mambobin majalisar wadanda suka fito daga bangarorin kasuwanci da ilmi suka gabatar da shawarwari kan yadda za a kara kyautata yanayin kasuwanci da kuma ingiza bunkasuwar tattalin arzikin dake shafar kamfanoni masu zaman kansu a kasar ta Sin. (Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China