Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Matsin Lamba Ba Zai Hana Ci Gaban Kasar Sin Wajen Yin Kirkire-kirkire Kan Kimiyya Da Fasaha Ba
2019-06-18 20:39:55        cri

Kwanan baya, Tu Youyou, wadda ta samu lambar yabo ta Nobel, kuma masaniya a fannin ilmin magani ta kasar Sin, ita da tawagarta sun sanar da sabon ci gaba da suka samu, inda suka gabatar da hakikanin shirin na warware batun rashin tasirin maganin artemisinin kan zazzabin malaria. Wannan ce sabuwar gudummowar da masanan kasar Sin suka bayar, wajen warware matsalolin ilmin likitanci da dan Adan ke fuskanta, da kyautata harkokin kiwon lafiya na duniya.

Amma, wasu Amurkawa suna damuwa sosai a kan irin kirkire-kirkiren da kasar Sin ke yi a fannin kimiyya da fasaha. Ba su yi tunani kan yaya za su karfafa karfin takara na kasarsu, da more irin nasara tare da kasashen duniya ba, a maimakon haka, suna tsayawa kan tayarwa, da kuma yada jita-jita, don bata sunan kasar Sin. A karshen watan Afrilun bana, shugaban hukumar bincike ta tarayyar Amurka (FBI) Christopher Wray, a yayin jawabinsa ya kara shafa kashin kaji ga kasar Sin na cewa, wai kasar Sin "ta karawa duk al'ummar kasar karfin gwiwar ikon satar mallakar fasaha ta hanyoyin kamfannoni, da jami'ai da hukumomi daban daban." Kwanan nan, kasar Amurka ta yi amfani da dalilinta na wai kiyaye "tsaron kasa", don hana daliban kasar Sin zuwa kasar Amurka yin karatu, da hana kamfanonin kasar Sin shiga kasuwar Amurka, da kuma amfani da ikon kasa don kawo cikas ga wasu kamfanonin kasar Sin, ciki har da kamfanin Huawei, kana ta sarrafa wasu kamfanonin kasar Amurka da dama, don dakatar da samar da kayayyaki ga kamfanonin kasar Sin, har ma wasu Amurkawa sun ce, za a katse dangantaka da Sin a fannin kimiyya da fasaha, da nufin tabbatar da matsayin koli na kasar Amurka a fannonin kimiyya da masana'antu.

Mujallar Bloomberg Businessweek, ta wallafa wani rahoton dake cewa, a 'yan shekarun nan, gwamnatin Amurka na yunkurin cin zarafin masana kimiyyar kasar Sin, sakamakon tsoron da take ji na kasar Sin, na cewa Sin ta "sace" fasahohin zamani na Amurka, duk da cewa babu kwararan shaidun dake nuna cewa wadannan masana kimiyyar Sin sun yi hakan. Wannan rahoton ya nuna cewa, kasar Amurka wadda ta dade tana mallakar fasahohin zamani da yawa tana jin tsoron shiga takara tare da sauran kasashe, wato Amurka na nuna matukar damuwa da rashin yarda da kanta, gami da jin tsoro a wasu fannonin fasaha, al'amarin da ya sa take yunkurin cin zarafin abokan hamayyarta ta hanyar nuna fin karfinta a bangaren fasaha. Amurka ta yi biris da ka'idoji, gami da dokokin kasa da kasa, kana ba za ta yarda da ci gaban sauran wasu kasashe ba.

Amma duk da haka, babu wanda zai iya hana ci gaba, gami da kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha na kasar Sin. A tarihin Jamhuriyar Jama'ar kasar Sin, ko da lokacin da kasar ke cikin mawuyacin halin tattalin arziki, da fuskantar takunkumi daga kasashen yammacin duniya, ta yi kokarin kirkiro wasu manyan boma-bomai biyu, gami da wani tauraron dan Adam. Bayan da ta fara aiwatar da manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje, ya zuwa yanzu, miliyoyin ma'aikatan kimiyya da fasahar kasar Sin na nuna azama wajen yin kirkire-kirkire ga fasahohin zamani, da bayar da babbar gudummawa wajen warware matsalolin dake addabar dukkan bil'adama a duniya.

Alal misali, Sin ta gano maganin artemisinin, wanda ya taimaka wajen bada jinya ga masu kamuwa da cutar malaria fiye da miliyan daya na kasashen Afirka. Da "Hybrid rice" nau'in irin shinkafa mai yabanya da yawa ya warware matsalar yunwa dake addabar mutane fiye da miliyan 100 a duniya. Tauraron dan Adam mai suna "Chang'e-4" ya sauka a duniyar wata karo na farko, wanda ya taimakawa dan Adam wajen kara sanin duniyar wata.

A gun dandalin tattaunawa kan tattalin arzikin duniya da aka gudanar a birnin St. Petersburg a kwanakin baya, shugaban kasar Sin ya bayyana cewa, Sin tana son more sabbin fasahohin kimiyya da nazari, ciki har da fasahar 5G ga kasa da kasa, wanda zai taimakawa kasa da kasa su kara karfi na canja tsarin bunkasar tattalin arziki.

A halin yanzu, Sin ta samu kwararru fiye da miliyan 170, kudin da aka zuba a fannin yin nazari ya kai matsayi na biyu a duniya, kana yawan mallakar fasaha da aka nema, da kuma samun izinin yin amfani ya kai matsayin farko a duniya. Firaministan kasar Malaysia Mahathir Bin Mohamad ya bayyana a fili a kwanakin baya cewa, bai kamata Amurka ta so kiyaye zama matsayin farko a fannin kimiyya da fasaha har abada ba, maimakon haka ya kamata ta amince Sin ta samu ci gaba a wannan fanni.

Isaac Newton ya taba bayyana cewa, dalilin da ya sa ni hange nesa shi ne, na tsaya a kan kafadar mutane masu tsayi. Amurka ta samu nasarori a fannin kimiyya da fasaha bisa tushen kirkire-kirkiren da aka yi a lokacin da. Amma a halin yanzu, wasu 'yan kasar Amurka sun manta da dalilin da ya sa Amurka ta samu karfi, sun fara yin amfani da hanyar hana bunkasuwar sauran kasashen duniya a fannin kimiyya da fasaha. Sai dai kuma hakan zai kara sa kaimi ga Sin da sauran kasashen duniya, su yi imani da ci gaba, da yin kirkire-kirkire, da kara samun bunkasuwar kimiyya da fasaha. A karshe, za a bar Amurka a baya, yayin da ake kokarin bunkasa kimiyya da fasaha a duniya. (Bilkisu Xin, Murtala Zhang, Zainab Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China