Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wajibi ne shirye-shiryen wanzar da zaman lafiya na MDD su kiyaye dokokin majalisar
2019-06-19 10:44:53        cri

Mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Wu Haitao, ya ce wajibi ne shirye-shiryen wanzar da zaman lafiya na MDD su kiyaye ka'idoji da manufofin majalisar da na ayyukan wanzar da zaman lafiya.

Wu Haitao ya shaidawa kwamitin sulhu na MDD cewa, dole ne a girmama cikakken 'yanci da shugabancin kasashen da ke karban bakuncin shirye-shiryen.

Ya kara da cewa, dole ne a ba da muhimmanci ga tuntubar kasashen da bangarori masu ruwa da tsaki, domin samun yardarsu a dukkan matakan tura jami'ai. Yana mai cewa, dole ne a magance matsalolin da suka shafi ayyukan a kan lokaci, kuma ta hanyar tuntuba.

Wu Haitao ya ce, akwai bukatar taimakawa kasashen wajen ginawa da inganta hukumominsu da kara karfin al'ummarsu.

A cewarsa, ayyukan wanzar da zaman lafiya, muhimman hanyoyi ne na tabbatar da zaman lafiya da tsaro a duniya, domin suna taka muhimmiyar rawa wajen daidaita matsalolin kasashen da karfafa karfinsu na tabbatar da tsaro. Sannan suna taimakawa wajen samar da yanayi mai kyau na warware matsaloli a siyasance. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China