Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Donald Trump ya kaddamar da yakin neman sake tsayawa takara a zaben 2020
2019-06-19 11:02:18        cri

Shugaban Amurka Donald Trump, ya kaddamar da yakin neman sake tsayawa takara a zaben shekarar 2020, a wani gangami da ya gudana daren jiya a birnin Orlando na jihar Florida.

A jawabin da ya gabatar, Donald Trump ya tabo batutuwa da dama, ciki har da tattalin arzikin kasar da dabarun gwamnatinsa kan batun shige da fice da na cinikayya da kuma kokarinsa na sake fasalin kotunan kasar.

Ya kuma soki wasu batutuwa da suka hada da, wadanda ke hamayya da shi da wasu manyan kafafen yada labarai da kuma bincike da aka yi kan batun sa hannun Rasha a zaben shekarar 2016, da aka kammala a watan Maris.

An zabi Donald Trump matsayin shugaban Amurka na 45 ne a shekarar 2016, inda ya doke Hillary Clinton, 'yar takarar jam'iyyar adawa ta Democrats.(Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China