Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kara buga harajin kwastam ga Sin zai haddasa karuwar farashin wayar salula da kamfuta na kasar Amurka
2019-06-19 15:16:45        cri

Bisa binciken da kamfanin bada shawara kan cinikin duniya na kasar Amurka ya yi, matakin Amurka na kara buga harajin kwastam ga kayayyakin sadarwa na Sin zai haddasa karuwar farashin wayar salula da kamfuta na kasar Amurka, wanda zai kawo babban tasiri ga masu sayayya na kasar Amurka.

Gwamnatin kasar Amurka tana son kara buga harajin kwastam ga kayayyakin Sin da darajarsu ta kai dala biliyan 300. Bisa rahoton da kamfanin bada shawara kan harkokin ciniki na duniya na kasar Amurka ya gabatar ga kungiyar kula da masu sayayya da fasahohi ta kasar Amurka a ranar 17 ga wata, an ce, idan aka kara buga harajin kwamtam din, masu sayayya na kasar Amurka za su kara kashe kudi dala biliyan fiye da 8.1 don sayen wayar salula, kana za su kara kashe kudi dala biliyan 8.2 wajen sayen kamfuta samfurin ta notebook da ta pad. Bayan da aka yi kidaya, za a samu hasarar dala biliyan 4.5 a fannin tattalin arzikin wayar salula, da dala biliyan 3.6 a fannin kamfuta samfurin ta notebook da ta pad. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China