Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD: Yawan yan gudun hijira a duniya ya kai matsayin koli a shekaru 70 da suka gabata
2019-06-20 10:15:39        cri

Hukumar kula da harkokin 'yan gudun hijira ta MDD ta gabatar da wani rahoto a jiya Laraba, wanda ya bayyana cewa, ya zuwa karshen shekarar 2018, yawan 'yan gudun hijira a duk fadin duniya ya kai miliyan 70.8, wanda ya ninka sau 20 bisa makamancin lokaci na shekaru 20 da suka gabata, adadin da ya kai matsayin koli a cikin shekaru 70 da suka gabata.

A cikin rahoton mai taken "Makomar duniya", hukumar ta yi bayani cewa, a shekarar 2018, yawan 'yan gudun hijira ya karu da miliyan 2.3.

Rahoton ya kuma ce, ya zuwa karshen shekarar 2018, yawan 'yan gudun hijira ya kai miliyan 25.9, sakamakon yake-yake, rikice-rikice da kuma gallazawa da ake musu, adadin da ya karu da dubu 500 bisa na makamancin lokaci na 2017. A sa'i daya kuma, mutane kimanin miliyan 3.5 na kokarin neman mafaka a ketare, sauran mutane miliyan 41.3 kuwa, suna gudun hijira cikin kasashensu.

Babban jami'in hukumar Filippo Grandi, ya shedawa manema labarai cewa, yawan 'yan gudun hijira yana ci gaba da karuwa ne a duniya sakamakon yake-yake da rikice-rikice da dai sauran dalilai, wanda ya kasancewar daya daga wasu matsalolin da duniya ke fuskantar mafi tsanani a halin yanzu. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China