Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An bude bikin nune-nunen fim na kasar Sin na shekarar 2019 a Nijeriya
2019-06-20 10:57:36        cri

A ranar 18 ga wata da dare, aka bude bikin nune-nunen fim na kasar Sin na shekarar 2019 a birnin Abuja dake kasar Nijeriya, taken bikin shi ne "dunkulewar kasa da kasa ta hanyar shawarar 'ziri daya da hanya daya'".

Mashawarci mai kula da al'adu na ofishin jakadancin Sin dake Nijeriya Li Xuda ya bayyana a wajen bikin budewar cewa, Nollywood na kasar Nijeriya shi ne cibiyar samar da fina-finai ta biyu a duniya, yanzu ana kokarin raya sha'anin fim na kasar Sin, ana fatan Sin za ta kasance kasuwa mafi girma ta fim a duniya. An yi imanin cewa, za a sa kaimi ga yin mu'amala da hadin gwiwa a tsakanin Sin da Nijeriya a wannan fanni ta hanya gudanar da bikin nune-nunen fim na Sin a kowace shekara.

A nasa bangare, mataimakiyar ministan harkokin sadarwa da al'adu da yawon shakatawa ta Nijeriya Grace Isu Gekpe ta yi jawabi ta hannun wakilinta Ugochi Akudo-Nwosu cewa, a cikin shekarun baya baya nan, Nijeriya da Sin sun yi mu'amala da hadin gwiwa sosai a fannin al'adu, kana an samu babban ci gaba a wadannan shekaru. Tana fatan za a nemi sabbin hanyoyin zurfafa hadin gwiwarsu da yin mu'amalarsu a fannin fim ta hanyar gudanar da bukukuwan nune-nunen fim da juna. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China