Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Bikin fina-finan kasa da kasa na birnin Shanghai yana taimakawa cudanyar al'adu tsakanin kasashe daban daban
2019-06-20 14:21:59        cri

Yanzu a birnin Shanghai dake gabashin kasar Sin, ana gudanar da wani bikin fina-finan kasa da kasa, lamarin da ya janyo hankalin kasashe da yawa, tare da ba su damar yin cudanyar al'adu.

Bikin fina-finan dake gudana a birnin Shanghai a wannan karo, ya janyo hankali kasashe fiye da 50, da shawarar "Ziri Daya da Hanya Daya" (BRI) ta shafa, wadanda suke halarci bikin da fina-finansu fiye da 1800.

Idan mun waiwayi baya, za mu ga cewa, a wajen bikin fina-finai na Shanghai na shekarar 2018, an kafa wani kawancen bukukuwan fina-finai karkashin shawarar "Ziri Daya da Hanya Daya", wanda ya kunshi hukumomin masu tsara bikin fina-finai 31 na wasu kasashe 29. A cikin shekarar da ta gabata, mambobin kawancen sun yi kokarin hadin gwiwa da juna, yayin bikin fina-finai na Shanghai shi ma ya taimaka wajen gabatar da fina-finai masu kyau na kasar Sin zuwa ga masu sha'awar fina-finai na sauran kasashe.

A bana, an kara habaka kawancen bukukuwan fina-finan da karin wasu mambobinsu guda 7, wadanda suka hada da bikin fina-finai na Rome na kasar Italiya, da bikin fina-finai na Kiv na kasar Ukraine, da dai makamantansu. Habakar ta sa yawan mambobin kawancen ya kai 38, wadanda suka kasance hukumomi masu tsara bikin fina-finai na wasu kasashe 33.

Dangane da batun na halarci wannan kawance, Francesca Via, shugabar bikin fina-finai ta Rome na kasar Italiya, ta ce,

"Muna wakiltar kawancen bukukuwan fina-finai na shawarar 'Ziri Daya da Hanya Daya'. A ganina, yadda muka halarci kawancen yana da muhimmanci sosai, domin ta haka ne za mu samu damar mu'amala da sauran kasashe. Yanzu mun samu damar kara sanin al'adun fina-finai na sauran kasashe. Wannan dama tana da muhimmanci matuka."

Kasuwar fina-finai ta kasar Sin tana kara samun ci gaba cikin sauri a shekarun baya bayan nan, inda fina-finan kasar da dama suka samu karbuwa a kasashe daban daban. A ganin shugaban bikin fina-finai na Warsaw na kasar Poland, Stefan Laudyn, kasar Sin na da dimbin labaran da za a iya tsarawa zuwa fina-finai. A cewarsa,

"Yawan al'ummar kasar Sin ya kai biliyan 1.3, wannan na nufin a kalla akwai labarai biliyan 1.3 da ake bayyana su a ko da yaushe. Ya kamata a bayyana labaran na Sinawa."

Tun bayan da aka fara nuna wasu fina-finai masu alaka da "Hanyar Siliki", wadda ita ce tsohuwar hanyar ciniki da ta hada kasar Sin da sauran kasashen dake yammacinta, a shekarar 2015, bikin nuna fina-finan kasa da kasa na Shanghai na ta kokarin samar da damammaki domin kasashe masu alaka da shawarar "Ziri Daya da Hanya Daya" su yi cudanya a fannin al'adun fim. A bana, cikin dukkan fina-finai kimanin 4000 da ake nuna su a birnin Shanghai, kusan rabinsu na kasashe masu alaka da shawarar "Ziri Daya da Hanya Daya" ne. Za a iya ganin wani babban ci gaba a wannan fanni, idan an kwatanta da jimillar shekarun baya.

Sa'an nan, game da amfanin da bikin nuna fina-finan ke tare da shi, Madam Fu Wenxia, darektar cibiyar bikin fina-finan kasa da kasa ta birnin Shanghai, ta ce,

"Tarihin fim ya kai fiye da shekaru 100, yayin da tarihin bikin fim ya kai shekaru 70. Bikin yana da amfani sosai ga ayyukan shirya fina-finai, gami da sana'ar baki daya. Sai dai abu na farko da ya kamata a maida hankali kansa shi ne a kara cudanya tsakanin al'adu daban daban, da gabatarwa karin jama'a da fina-finai masu inganci sosai."

Tsakanin ranar 15 da 24 ga watan Yuni, da ake gudanar da bikin fina-finai na Shanghai, za a nuna wasu fina-finai na kasar Sin da na kasashen waje kimanin 500 cikin gidajen siniman birnin Shanghai. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China