Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yin shawarwari cikin adalci ne hanya kadai da za'a iya bi wajen daidaita sabani tsakanin Sin da Amurka
2019-06-20 19:32:02        cri

Shugabannin kasashen Sin da Amurka, sun zanta ta waya a shekaranjiya 18 ga wata, inda suka bayyana cewa, za su sake ganawa da juna a yayin taron kolin G20 wanda za'a yi birnin Osakar kasar Japan, da amincewa da kara mu'amala tsakanin tawagogin tattalin arziki da cinikayya na kasashensu, al'amarin da ya rage damuwar duniya, da farfado da kasuwar hannayen jarin duniya.

Duba da tsanantar takaddamar cinikayya, da rashin sanin tabbas game da tattalin arzikin duniya, hukumar WTO ta rage hasashen da ta yi kan karuwar kasuwancin duniya na bana daga kaso 3.7 zuwa 2.6 bisa dari. Bankin duniya ma ya fitar da rahoto, inda ya rage habakar tattalin arzikin duniya na bana da na badi, zuwa kaso 2.6 da kaso 2.7 bisa dari. Domin taimakawa ci gaban tattalin arzikin duniya da kare hakkin al'umma, Sin na maida yin shawarwari a gaban komai, da kara tuntubar kasar Amurka, a kokarin lalubo bakin zaren daidaita takaddamarsu tun da wuri.

Akwai bukatar a yi hadin kai da shawarwari bisa manufa. Muhimmin abu wajen shawarwarin tattalin arziki da cinikayya a tsakanin kasashen Sin da Amurka, shi ne a yi kokarin cimma burin bai daya. Ya kamata a yi tattaunawa cikin zaman daidai wadaida, bisa muhimmin ra'ayin bai daya da shugabannin kasashen biyu suka cimma a karshen shekarar bara, a Argentina, kuma bisa tushen nuna girmama ga juna, da samar da moriya ga juna, kana da kulawa, da damuwa masu dacewa da suke nunawa juna.

Bayan wayar tarho a tsakanin shugabannin biyu, wakilin Amurka dake kula da harkokin cinikayya Robert Lighthizer, ya bayyana ra'ayinsa mai ban mamaki a yayin da yake ba da shaida a majalisar dokokin kasar. A yayin da yake ba da shaida ga kwamitin kudi na majalisar dattawa, ya bayyana cewa, ba za a iya warware matsala ta hanyar yin shawarwari kadai ba. Game da tambayar da aka yi masa cewa, idan an yi hasara kan shawarwari a tsakanin Amurka da Sin, to yaya za a yi? Robert Lighthizer ya ba da amsa cewa, har zuwa yanzu ba a samu dabarar da ta fi kyau bisa ta kara sanya haraji ba. A yayin da yake ba da shaida ga kwamitin tattara kudi na majalisar wakilai, ya bayyana cewa, ya kamata a warware matsaloli ta hanyar kyautata dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, da kuma kiyaye matsayin fifiko na takara na kasar ta Amurka.

Ra'ayin Robert Lighthizer na baya da na yanzu sun nuna cewa, a wani bangare, Amurka na son sake yin shawarwarin cinikayya a tsakanin Sin da Amurka domin kyautata dangantakarsu, amma a wani bangaren daban, Amurka na da aniyar saka wa kayayyakin Sin kudin haraji. Babu shakka wannan ba ra'ayi ba ne da ya dace da warware matsala kwata kwata.

"Girmamawa juna, da rike amana, da zaman daidaito, da moriyar juna" muhimman kalamai ne da Sin ke mai da hankalinta a kai, yayin da take shawarwari tare da Amurka. Ya zuwa yanzu dai, ya kamata Amurka ta san muhimman batutuwan da Sin ke lura da su, da kuma batutuwan da dole ne Sin ba za ta yi rangwame a kai ba.

Akwai sauran kwanaki kasa da 10 kafin ganawar shugabannin Sin da Amurka a garin Osaka. Ana fatan tawagogin tattalin arziki da cinikayya na bangarorin biyu, za su ci gaba da hada kansu bisa muhimmin ra'ayi bai daya da shugabannin biyu suka cimma a kasar Argentina, a kokarin warware sabanin da ke tsakaninsu. Idan Amurka za ta ci gaba da yin shawarwari, tare da daga kudin harajin gaba daya, to ba za a samu kyakkyawan sakamako ba. Sin da Amurka ba za su iya samun daidaito a tsakaninsu ba, sai sun tsaya tsayin daka kan yin tattaunawa cikin adalci, da lura da batutuwan da suke mai da hankulansu a kai.(Masu fassarawa: Murtala, Bilkisu, Kande)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China