Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An bude taron Ilimin sana'o'i tsakanin Sin da Afirka a Uganda
2019-07-05 10:31:28        cri
A jiya ne karamin ministan ilimi mai zurfi na kasar Uganda John Chrysestom Muyingo, ya bude taron karawa juna sani game da musayar ilimin sana'o'i tsakanin kasar Sin da Afirka na shekarar 2019, taron da ya samu halartar masana Ilimi daga kasashen Sin da Kenya da Tanzaniya da Habasha gami ga Uganda mai masaukin baki.

Yayin taron mai taken " gina kyakkyawar makoma ta bai daya ga daukacin bil-Adama da gina makoma mai haske ga ilimin sana'o'i na kasashen Sin da Afirka, ana sa ran mahalartansa za su tattauna yadda ilimin sana'o'i zai hanzarta raya nahiyar Afirka.

A wasikar da ya aikewa taron, mataimakin babban darektan cibiyar musaya tsakanin al'ummomin kasa da kasa ta kasar Sin a ma'aikatar Ilimin kasar Yang Xiaochun, ya ce, yana fatan za a tsara matakai tare da bullo da hanyoyi na hadin gwiwar ilimin sana'o'i tsakanin Sin da kasashen dake gabashin Afirka.

Taron na kwanaki biyu, ya samu halartar cibiyoyi 16 daga kasar Sin da kuma 40 daga Afirka.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China