Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Tattalin arziki mai zaman kansa ya samu ci gaba cikin lumana a birnin Wenzhou
2019-08-04 14:34:06        cri

Tun farkon lokacin da aka fara aiwatar da manufar yin gyare-gyare a cikin gida da kuma bude kofa ga kasashen ketare a nan kasar Sin wato a shekarar 1978, sai tattalin arziki mai zaman kansa na birnin Wenzhou ya fi saurin samun ci gaba idan aka kwatanta da sauran yankunan kasar, har ya kai sahun gaba a fadin kasar, yanzu haka an shiga sabon zamani, birnin ya rasa fiffikonsa a bangaren raya tattalin arziki mai zaman kansa, hakika wasu sauran biranen kasar sun riga sun maye gurbinsa a fannin, dalilin da ya sa haka shi ne domin akwai wahala game da dabarun raya tattalin arzikin da ake amfani da su su iya biyan sabbin bukatu a yanayin da ake ciki yanzu, misali kirkire-kirkiren tsarin tattalin arziki, da kirkire-kirkiren fasahohi, da ingantattun sana'o'i, har wasu manyan kamfanoni masu zaman kansu za su canja shugabanninsu, wato matasa za su fara rike ikon tafiyar da harkokin kamfanonin a maimakon tsoffin shugabannin da za su yi ritaya.

A karkashin irin wannan yanayin da ake fuskantar, gwamnatin birnin Wenzhou ta fitar da wata sabuwar manufa domin rage matsin lambar da ake yiwa kamfanonin, tare kuma da rage kudin da suke bukata yayin da suke gudanar da harkokinsu, ta yadda za a taimakawa ci gabansu yadda ya kamata.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China