Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Muhimmancin yarjejeniyar AfCFTA ga ci gaban Afirka
2019-07-18 09:07:50        cri

A ranar Lahadi 8 ga watan Yulin wannan shekarar ce, shugabannin kasashen Afrika suka kaddamar da fara aiki da yarjejeniyar ciniki maras shinge ta kasashen Afrika wato (AfCFTA) a hukumance a birnin Niamey na Jamhuriyar Nijar.

An fara aiki da yarjejeniyar ce a lokacin kaddamar da taron kolin shugabanin kasashen mambobin kungiyar (AU) karo na 12 da ya guda a birnin nan Niamey.

Shugaban gudanarwa kungiyar AU, Moussa Faki Mahamat, ya yaba da kaddamar da yarjejeniyar, inda ya bayyana cewa, tana da muhimmanci a tarihin kasashen Afrika, musamman a yunkurin tabbatar da burin ajandar shekaru 50 ta raya nahiyar Afrika nan da shekarar 2063.

Shugaban kasar Masar Abdel Fattah al-Sisi, shugaban karba-karba na kungiyar AU na wannan karo, ya bayyana ranar a matsayin mai muhimmanci ga yunkurin Afrika na neman bunkasa ciniki da kasuwanci da dunkulewar nahiyar

Mataimakiyar babban sakataren MDD Amina Mohammed ta ce, fara aiki da yarjejeniyar ciniki maras shinge al'amari ne mai cike da tarihi ga Afrika. Sai dai ta bukaci kasashen Afrika su yi kokarin cin gajiyar dake tattare da shirin yarjejeniyar cinikin.

An kaddamar da yarjejeniyar ta AfCFTA ce, a ranar 21 ga watan Maris a bara a Kigali, babban birnin kasar Rwanda, kuma a ranar Lahadin ne Najeriya kasa mafi yawan al'umma da karfin tattalin arziki a nahiyar Afrika, da jamhuriyar Benin suka rattaba hannu kan yarjejeniyar, yayin da Eritrea ce kasa daya tilo cikin mambobin kungiyar tarayyar Afrika 55 da ba ta sanya hannu kan yarjejeniyar ba kawo yanzu

Masana harkokin tattalin arziki na cewa, idan ana son cimma burin yankin ciniki maras shinge na Afrika, akwai bukatar kasar Sin ta taimaka wajen gina ababen more rayuwa da ake bukata domin gudanar da harkoki cinikayya a nahiyar. A karshe ita ma kasar Sin za ta amfana daga fadadar tattalin arzikin nahiyar dake da ingantacciyar dangantakar cinikayya da ita.

Yankin ciniki maras shinge na nahiyar zai samar da moriyar juna tsakanin masu sarrafa kayayyaki da masu sayyayya. Kana cinikayya za ta taimakawa kasashen Afrika samun ci gaba cikin sauri, za ta kuma iya bunkasa cinikayyar da kasar Sin, saboda yanzu kasashen Afrika za su samu ci gaban da zai kai su ga yin harkokin sayayya a wajen nahiyar.

Karuwar cinikayya tsakanin kasashen Afrika, za ta fadada tattalin arzikin nahiyar, wanda kuma zai taimaka ga inganta cinikayya tsakaninta da kasashe kamar Sin. (Ahmed, Saminu, Ibrahim /Sanusi Chen)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China