Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shirin yaki da cutar HIV a Botswana ya samu gagarumar nasara wajen hana yaduwar cutar
2019-07-21 15:39:29        cri

Wani nazarin bincike na jami'ar Harvard ya nuna cewa shirin yaki da cuta mai karya garkuwar jiki wato HIV a kasar Botswana ya samu gagarumar nasara, inda aka samu raguwar kamuwa da cutar a bisa matsayin kolin.

Rahoton binciken wanda aka wallafa a mujallar kiwon lafiya ta New England Journal of Medicine ya nuna cewa, kwayar cutar ta fara raguwa, kuma a halin yanzu, ba'a iya yada kwayar cutar a tsakanin manyan mutane mazauna sassan kasar, kana marasa lafiyar dake fama da cutar suna samun ingantacciyar kulawa.

Haka zalika, shirin yaki da cutar ya bada gudunmawar kusan kashi 1 bisa 3 na raguwar kamuwa da kwayoyin cutar a wasu yankuna 15 na kasar, kamar yadda rahoton binciken ya nuna.

Wani shehun malami a sashin nazarin kwayoyin cututtuka na jami'ar Harvard, Shahin Lockman, ya ce, an cimma gagarumar nasara wajen gwaje-gwajen kwayar cutar HIV, da magance cutar, da kuma hana yaduwar cutar tsakanin jama'a wanda shi ne rahoton ci gaba mafi girma da aka samu a duniya baki daya.

Yaduwar cutar HIV a Botswana ya yi matukar kamari, an kiyasta kashi 23 bisa 100 na mutane manya a kasar na dauke da cutar HIV a bisa nazarin bincike a shekarar 2017. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China