Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ye Shiwen ta lashe azurfa a gasar linkaya ajin mata ta FINA
2019-08-01 08:47:19        cri


'Yar wasan linkaya ta kasar Sin Ye Shiwen, ta lashe lambar azurfa a gasar linkaya ajin mata ta mita 400 wadda hukumar FINA ke shiryawa.

A karshen mako ne dai aka kammala gasar wasannin linkayar, inda Ye ta kammala iyo cikin mintuna 4:32.07, minti 1.68 bayan Katinka Hosszu daga kasar Hungary, wadda ita ce ta yi na daya, ta kuma lashe lambar zinari bayan ta kammala iyo cikin mintuna 4:30.39.

'Yar wasan ta kasar Sin, ya wuce Yui Osashi daga kasar Japan, suna daf da kammala iyo, inda daga karshe Osashi ta zo ta uku da lambar tagulla, bayan da ta kammala iyo cikin mintuna 4:32.33.

Da take jawabi bayan kammala gasar, Ye mai shekaru 23 da haihuwa, ta ce "na yi matukar kokari a wannan yammaci. Har kullum ina jin tsoron wannan gasa, amma dai na yi iya yi na, na kallama iyon mita 400, wanda hakan ya tabbatar min zan iya,". Ta ce "A yayin gasar, na yi kokarin shawo kan abubuwan da nake tsoro. A yau, ina jin nutsuwa a rai na, zan kuma rika murmushi ma kafin fara wata gasar,".

Baya ga wannan nasara da ta samu, har ila yau, yayin dai wannan gasa, Ye ta lashe lambar azurfa a iyon mita 200 na daidaikun 'yan wasa.

Kana a can baya ta taba lashe lambar zinari a iyon mita 200 da 400 na daidaikun 'yan wasa, a gasar Olympic ta shekarar 2012(Saminu, Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China