Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kafar yada labarai ta Singapore: Babu alakar kasar Sin da matsalar da Amurka ke ciki na amfani da magungunan Opioids
2019-08-19 14:06:51        cri
Kwanan baya, tsohon babban direktan jaridar The Straits Times ta Singapore Leslie Fong, ya wallafa wani bayani a jaridar mai taken "Ko akwai dangantaka tsakanin haraji, magungunan Opioids da tabar wiwi", inda ya bayyana cewa, shugaba Donald Trump ya fake da zargin wai kasar Sin ba ta hana shigar da maganin kashe zafi na Fentanyl cikin Amurka wajen kara bugawa kasar Sin haraji, kana ya alakanta matsalar amfani da magungunan Opioids ta hanyar da ba ta dace ba da Amurka ke fama da ita, da takaddamar ciniki a tsakanin wadannan kasashen biyu mafiya girma ta fuskar tattalin arziki. Lallai lamarin ya ba mutane matukar mamaki.

Bayanin ya kuma nuna cewa, barkewar wannan matsala a Amurka na da alaka da kamfanoni masu samar da irin wadannan magungunan, wadanda ba su yi gargadi kan yiyuwar illar da ke tattare da shan wadannan magunguna ba, har ma suka zuga likitocin da su kara bayar da su. Hakan ya sa, gwamnatin Amurka ba ta iya kayyade yin amfani da su yadda ya kamata ba, kafin barkewar matsalar da ba za a iya magance ta ba.

Dadin dadawa, bayanin ya ce, yadda Amurka ta sauke da kuma dora wannan alhaki a wuyan kasar Sin, abu ne da ba shi da hujja ko dalili, illa dai munafunci ne dake zuciyarta. Ya ce Sin ta yi duk abin da ya dace kan batun maganin Fentanyl, babu wani dalilin da ya sa Amurka ta yi tir da ita kan matsalar. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China