Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ma'aikatar cinakayyar Amurka ta karawa kamfanin Huawei wa'adin kwanaki 90
2019-08-20 10:09:39        cri

Ma'aikatar cinakayya ta Amurka, ta ce an amince da karawa kamfanin Huawei na kasar Sin wa'adin kwanaki 90, na amfani da lasisin gudanar da hada hada tare da sauran kamfanonin Amurka, tare da jingine takunkumin da kasar ke shirin kakabawa kamfanin.

Wata sanarwa da ma'aikatar ta fitar ta ce, lasisin na wucin gadi, zai baiwa Hauwei zarafin gudanar da wasu kebantattun harkoki da suka kunshi cudanyar kasuwanci mai nasaba da shige da ficen hajoji, da musayar kayayyaki tsakanin kamfanin da wasu takwarorin da ba na Amurka ba.

Da yake tsokaci game da hakan, sakataren cinikayyar Amurka Wilbur Ross, ya ce karawa kamfanin wa'adin gudanar da harkokin sa, zai ba da damar kaucewa tsayawar al'amura.

Wannan mataki dai na zuwa ne yayin da abokan cinikayyar kamfanin na Huawei dake Amurka, musamman na yankunan karkara ke daf da fara fuskantar wahalhalu, idan har kamfanin ya dakatar da samar masu da hidimomi.

A daya bangaren kuma, hukumar dake lura da masana'antu da tsaro ta Amurka ko BIS a takaice, wadda ke karkashin ma'aikatar cinikayyar Amurka, ta sanya karin sassa 46 dake mu'amala da kamfanin Huawei cikin jerin sassa da ba su da tabbas ta fuskar cinikayya.

Sai dai a nasa bangare, kamfanin Huawei ya fitar da wata sanarwa a ranar Litinin, yana mai cewa, ko shakka babu, wannan matakin da aka ayyana, musamman a irin wannan lokaci yana da nasaba da siyasa, kuma ba shi da wata alaka da tsaron kasa. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China