Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jakadan Sin a batun kasar Sham ya bukaci daukar matakan da suka kamata na warware rikici ta hanyar siyasa
2019-08-21 10:43:51        cri
Jakadan kasar Sin game da batun kasar Sham ko Syria Xie Xiaoyan, ya yi kira ga sassan kasa da kasa, da su yi hadin gwiwa da juna, wajen tabbatar da bin hanyoyin da suka dace na warware rikicin Syria ta hanyar siyasa.

Bayan ganawarsa da wakilin musamman na MDD kan batun Syria Mr. Geir Pedersen a birnin Geneva a jiya Talata, Mr. Xie ya jaddada goyon bayan kasar Sin ga kudurin MDD na shiga tsakani, domin warware rikicin kasar ta Syria, da ma irin kwazon da Mr. Pedersen ke yi na cimma wannan buri.

Xie ya ce an samu ci gaba mai ma'ana a bangaren kafa kwamitin tsara kundin mulkin Syria, inda sassan masu ruwa da tsaki na kasar ke daf da kammala cimma yarjejeniya, wanda a ganin sa mataki ne da ya dace, wanda zai haifar da dama, ta kawo karshen rikicin kasar ta hanyar siyasa.

Daga nan sai jakadan na Sin ya sake jaddada cewa, Sin na goyon bayan aiwatar da matakin siyasa, wanda zai kai ga warware takaddamar mulki da ta dabaibaye Syria. Kaza lika tana goyon bayan tattaunar wanzar da zaman lafiya, da ci gaba da musayar ra'ayi, da tsara ganawa tsakanin masu ruwa da tsaki, tare da shiga a dama da ita a ayyukan wanzar da zaman lafiya masu kunshe da sabbin dabaru da shawarwari. (Saminu Hassan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China