Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yan sandan Uganda sun yi watsi da zargin amfani da na'urorin Huawei wajen leken asirin 'yan adawa
2019-08-21 10:50:28        cri
Rundunar 'yan sandan kasar Uganda, ta yi watsi da zargin amfani da na'urorin kamfanin fasahar kasar Sin Huawei, wajen leken asirin 'yan jam'iyyun adawar kasar.

A jiya Talata ne dai kafar "The Wall Street Journal" ta wallafa wani labari, wanda ke cewa, jami'an tsaron Uganda na amfani da kamfanin sadarwa na Huawei domin sanya ido kan 'yan adawar siyasar kasar.

Game da hakan, kakakin rundunar 'yan sandan kasar Fred Enanga, ya ce wannan zargi ne mai cike da mummunar manufa. Cikin wata nasarwar da aka fitar, Enanga ya ce zargin ba zai bata dangantar hadin gwiwa tsakanin kasar da kamfanin Huawei ba, kana ba zai taimakawa wajen cimma burin yada farfagandar yakin da wasu sassa suke yi, na neman mamaye kasuwar hajojin fasaha ba.

Fred Enanga ya kara da cewa, 'yan sandan kasar sun baiwa kamfanin Huawei kwangilar kafa na'urorin sa ido na CCTV a sassan kasar, a wani mataki na karfafa kare doka da oda. An kuma tanaji duk wasu matakai na nazari, da samar da kayan aikin da suka wajaba, karkashin managarcin tsarin fasaha da na aikin 'yan sanda.

Ya ce "muna tabbatarwa al'ummar kasar Uganda cewa, ba wani abun damuwa game da ayyukan fasaha da kamfanin Huawei ke gudanarwa. (Saminu Hassan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China