Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kamfanonin sarrafa takalma fiye da 200 na Amurka sun bukaci Trump da ya soke umurnin kara dora kudin haraji kan kayayyakin Sin
2019-08-30 16:16:53        cri

Kwanan baya, kamfanonin sarrafa takalma da masu dillancin takalma fiye da 200 na kasar Amurka, sun aike da wata wasika zuwa ga shugaba Donald Trump, inda suka yi kira da ya soke umurnin kara dora kudin haraji kan kayayyakin da kasar Sin ke sayarwar a Amurka.

A cikin wannan wasikar, kamfanonin sun yi gargadin cewa, kara dora kudin haraji kan kayayyakin da Sin ke sayarwa Amurka zai tilasta wa masu sayayya na Amurka su kara biyan dalar Amurka biliyan 4 a ko wace shekara, tare da kara barazanar samun koma-bayan tattalin arzikin kasar. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China