Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Tattalin arzikin Beijing ya samu ci gaba cikin sauri cikin shekaru 70 da suka gabata
2019-09-16 17:02:19        cri

A cikin sabon shirinmu na "Allah daya gari bamban", za mu yi muku bayani kan yadda birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin ya samu ci gaban tattalin arziki cikin sauri, da yankin Zhongguancun na birnin wanda ya samu ci gaba matuka a bangaren kimiyya da fasaha.

Tun bayan da aka kafa jamhuriyar jama'ar kasar Sin a shekarar 1949 wato shekaru 70 da suka gabata, birnin Beijing ya samu manyan sauye-sauye daga dukkan fannoni, ya zuwa shekarar 2018, adadin GDP na birnin ya kai kudin Sin yuan biliyan 3000, alkaluman da aka fitar sun nuna cewa, tun daga shekarar 1953 zuwa shekarar 2018, matsakaicin karuwar adadin GDP na Beijing a ko wace shekara ta kai kaso 10.4 bisa dari, kana birnin ya samu babban sakamako a bangaren ci gaban tattalin arziki mai inganci.

Hakika bayan kokarin da aka yi a cikin shekaru 70 da suka gabata, tattalin arziki da zaman takewar al'ummar birnin Beijing sun samu ci gaba cikin sauri, kana hadadden karfin birnin ya dagu matuka, haka kuma rayuwar al'ummun birnin ita ma ta kyautata a bayyane har ta kai matsayin koli a tarihi.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China