Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masana kimiyyar Amurka sun nuna nuna adawa da matakin dakile masu nazari na ketare da gwamnatin kasarsu ta dauka
2019-09-06 19:34:07        cri

Kungiyoyin masana kimiyya, da na masana'antu, da na ba da ilmi 60 na Amurka, sun fitar da wata wasikar hadin gwiwa a ranar 4 ga wata, wadda cikinta suka yi kira ga gwamnatin Amurka, da ta daina dakile masu nazari na ketare, da kawo cikas ga hadin kai ta fuskar kimiyya ta kasa na kasa.

A cikin wannan wasika, masana kimiyyar Amurka da na ketare, sun nuna damuwa matuka kan sabuwar manufa, da matakan da gwamnatin ke dauka bisa sunan "rage hadarin tsaro". A ganinsu, wadannan matakai ba su da wani amfani, illa dai kawo cikas ga sana'ar kimiyya. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China