Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Henry Alfred Kissinger: Ya kamata Sin da Amurka su daidaita bambancin ra'ayinsu ta hanyar hadin kai
2019-09-07 16:35:43        cri

Tsohon sakataren harkokin wajen Amurka, Henry Alfred Kissinger ya aike da wani sakon bidiyo ga dandalin manyan jami'ai, dake tattaunawa kan ci gaban kasar Sin, wanda aka rufe yau Asabar a nan birnin Beijing. A cikin wannan bidiyo, Henry Alfred Kissinger ya bayyana cewa, nauyin dake wuyan kasashen biyu gaba daya shi ne, magance matsalar dake tsakaninsu lami lafiya ta hanyar hadin kai.

Ya kara da cewa, Sin da Amurka kasashe ne dake da karfi matuka a fannonin kimiyya da fasahar siyasa da tarihi, wadanda suke iya kawo alfanu ga ci gaba da zaman lafiyar duniya. Ya ce suna fuskantar kalubalen hadin kai sosai, saboda mabambanta tarihi da al'adu da suke da su. Amma, ya yi imanin cewa, Sin da Amurka na da nauyin dake wuyansu gaba daya, na tabbatar da zaman lafiya da ci gaban duniya, da warware matsalolin dake tsakaninsu ta hanyar yin hadin kai, saboda a cewarsa, ya ganewa idanunsa irin bunkasar dangantakar kasashen biyu cikin shekaru 40 da suka gabata.

Asusun nazarin ci gaban kasar Sin ne ya dauki bakuncin gudanar da taron karawa juna sani na dandalin na shekarar 2019, wanda ya gudana daga ranar 6 zuwa 7 ga watan nan a birnin Beijing, karkashin jagorancin cibiyar nazarin ci gaban kasar Sin ta majalisar gudanarwar kasar. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China