Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
WHO ta bukaci kasashe da su kashe a kalla kaso 1 cikin 100 na GDPn su a matakin farko na kiwon lafiya
2019-09-23 10:09:43        cri

Hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta bukaci dukkan kasashen duniya, da su kara a kalla kaso 1 cikin 100 na GDPn su cikin kudaden da suke kashewa a fannin kiwon lafiya a matakin farko, ta yadda za a cike gibin da ke akwai a bangaren lafiya tare da cimma manufofin lafiya da aka amince a shekarar 2015.

Wani rahoto da hukumar ta fitar, ya yi kiyasin cewa, karin dala biliyan 200 da ake kashewa duk shekara wajen inganta matakin farko na kiwon lafiya tsakanin kasashen dake samun kudaden shiga kalilan da matsakaici, zai taimaka wajen ceto rayukan mutane miliyan 60, karuwar matsakaicin shekarun rayuwa da shekara 3.7 nan da shekara 2020, zai kuma taimaka matuka ga ci gaban tattalin arziki da jin dadin jama'a.

Rahoton ya kara da cewa, kasashen za su iya yin haka, ta hanyar kara kudaden da suke kashewa a fannin lafiya baki daya, ko su canja alakar kudaden zuwa bangaren kiwon lafiya a matakin farko, ko su yi amfani da su a dukkan sassa. Lamarin da ke nuna cewa, a halin yanzu, galibin kasashe ba sa zuba isasshen jari a bangaren kiwon lafiya a matakin farko.

Koda ya ke, a cewar rahoton, kasashe matalauta, za su ci gaba da neman taimako daga waje, ta yadda za su yi kokarin inganta tsare-tsarensu na kiwon lafiya da ma hidimomin lafiya da suke baiwa al'ummominsu a fadin kasashensu.

A halin da ake ciki, hukumar lafiya ta duniya, ta yi kira ga dukkan kasashe, da su kara samar da hidimomin kiwon lafiya a kasashensu, musamman kasashe masu samun kudaden shiga kalilan da yankunan karkara da ke kurar baya a bangaren kayayyakin kiwon lafiya, da ma'aikatan lafiya da tsare-tsaren samar da kayayyaki da ma ingancin samar da kulawar lafiya.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China