Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin na adawa da cin zalin kamfanoninta da Amurka ke yi bisa wasu dokokinta
2019-09-26 20:24:35        cri

Dangane da takunkumin da kasar Amurka ta sanar da sanyawa wasu kamfanonin kasar Sin, da wasu daidaikun Sinawa, a yau Alhamis, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ne Geng Shuang, ya yi nuni da cewa, kasar Sin ba ta ji dadi ba, kuma tana adawa da yadda Amurka ta sanar da sanya takunkumi, kan wasu kamfanonin kasar Sin da wasu daidaikun Sinawa.

Kakakin ya kara da cewa, kullum kasar Sin na adawa da matsayin Amurka, na sanya takunkumi bisa ra'ayin nuna bangaranci, da aiwatar da dokokinta wajen daidaita harkokin kasa da kasa.

Sin na nuna kiyayya ga cin zalin kamfanoninta da yarda da Amurka ke yi bisa fakewa da wasu dokokin da take aiwatarwa a gida. Kaza lika Sin ta bukaci Amurka, ta dakatar da matakanta nan da nan. Kasar Sin ta riga ta dauki wasu matakai na wajibi, za ta kuma ci gaba da dauka, a kokarin kiyaye halastattun hakkokin kamfanoninta. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China