Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kungiyar "Angel Eyes" ta zama jagora ga makafi
2019-10-05 16:37:34        cri

A yayin da al'ummar kasar Sin ke murnar cika shekaru saba'in da kafa Jamhuriyar Jama'ar kasar, a cikin shirinmu na yau, za mu ci gaba da kawo muku wani bayani game da nasarorin da kasar ta samu a wadannan shekaru, musamman a fannin kyautata zaman rayuwar mutanen da suke da bukata ta musamman.

A birnin Handan na lardin Hebei dake arewacin kasar Sin, akwai wata malama wadda ta shafe shekaru 13 tana bayyanawa makafi yadda fina-finai suke, da taimaka musu wajen tafiyar da sana'o'i, da inganta zaman rayuwa. Sunan malamar Kong Yuanyuan, mataimakiyar shugaba ce a sashin tsara fina-finai na gidan rediyo da talabijin na birnin Handan, kana shugabar kungiyar masu aikin sa-kai dake taimakawa makafi mai suna "Angel Eyes", wadda da Hausa ke nufin "Idanun Mala'ika" saboda yadda membobin kungiyar ke fatan kasancewa tamkar idanu ga makafi da suke baiwa hidimar kallon fina-finai.

A watan Yulin shekara ta 2006, madam Kong Yuanyuan ta jagoranci wata kungiyar masu aikin sa-kai zuwa wurare daban-daban na birnin Handan a lardin Hebei, don tallata ra'ayin kiyaye muhallin halittu, ta hanyar gabatar da wasanni masu kayatarwa, inda ta gamu da wasu makafi uku. Madam Kong ta ce:

"Mun ga akwai wasu mutane uku wadanda ke boye a can, ashe makafi ne su. Mun tambaye su, don me ba su zo wurin wasanni tare da sauran mutane ba, sun ce ba su so. Da muka tambaye su meye suke so, sun ce suna son kallon sinima."

Kong Yuanyuan da kungiyarta ba su taba tsammanin makafi su ma suna da bukatar kallon sinima ba. Ba da jimawa ba sai suka tuntubi ofishin watsa fina-finai na wurin, inda ya watsa fim din farko a wajen, aka kuma gayyaci makafi su sha kallo. Amma ba su gamsu sosai ba, har ma sun gayawa Kong Yuanyuan cewa, akwai wurare da dama a fim din da ba su gane ba ta hanyar sauraren sautinsa kawai.

Madam Kong da kungiyarta sun fahimta cewa, idan ana so a nunawa makafi fim, bai kamata a bar su su ji da kunnuwansu kawai ba, ya zama dole a bayyana musu meye abun dake faruwa a fim din yayin da ake nuna shi. Daga nan ne kuma Kong Yuanyuan ta fara daukar masu aikin sa-kai don kafa wata kungiya, da nufin bayyanawa makafi abubuwan dake faruwa a cikin fina-finai. Sunan kungiyar "Angel Eyes".

Daga shekara ta 2006 ya zuwa yanzu, a cikin shekaru 13, mutane masu aikin sa-kai a kungiyar "Angel Eyes" sun bullo da dabaru daban-daban don taimakawa makafi su gane abun dake faruwa a cikin fina-finai, wato a yi bayani filla-filla a wurare daban-daban, yayin da ake nuna fim din. Madam Kong ta ce:

"Tun farkon farawa, muna da masu aikin sa-kai guda bakwai ne cakal, wadanda suke iya bayyana abun dake faruwa a cikin fina-finai. A lokacin, mu kan rufe idanunmu baki daya a duk tsawon rana. Duk inda muka je, ba ma ganin komai, tamkar mu makafi ne. Idan abokanai sun zo wajenmu, sai mu maida su tamkar makafi ne su ma, inda mu kan yi mu'amala da juna tamkar mu'amalar makafi. Hakan ya sa muka kara fahimtar ainihin zaman rayuwar makafi."

Kawo yanzu, kungiyar masu aikin sa-kai dake bayyana fina-finai ga makafi ta "Angel Eyes" a birnin Handan tana da masu aikin sa-kai sama da dari bakwai, wadanda suka bayyana fina-finai masu ma'ana 45 ga makafi. Amma watakila abun da ba ku sani ba shi ne, a kan dauki tsawon lokaci ana shirya bayyana fina-finai ga makafi. Feng Yan na daya daga cikin masu aikin sa-kai a kungiyar "Angel Eyes", wadda ke kula da aikin zabar fina-finai wadanda suka dace da bukatar makafi, inda ta ce:

"Zabar fina-finai wadanda suka dace da makafi, na farko, ya kamata a zabi fina-finai da za su karfafa musu gwiwa, wato makafin za su iya amincewa da su cikin sauki. Na biyu, ya fi kyau a nuna musu fina-finai masu sauki, kana kuma bai kamata sautin fina-finai ya yi saurin gaske ba. Makasudinmu shi ne, ta hanyar bayyana musu fina-finai, makafin za su samu kwarin-gwiwa ga zaman rayuwarsu na yau da kullum."

Bayan da aka zabi fina-finai masu dacewa, madam Kong Yuanyuan da membobin kungiyarta, su kan yi nazari sosai kan abubuwan dake cikin fina-finan, sa'annan za su zabi wanda zai bayyana fim ga makafin daga cikin masu aiki sa-kai a kungiyar bisa la'akari ga muryarsa. Kungiyar masu aikin sa-kai ta "Angel Eyes" na da membobi 32 wadanda suka iya bayyana fina-finai ga makafi, ciki hadda maza biyu kacal, Li Jinglong na daya daga cikinsu. Bayan da ya shafe tsawon shekaru da dama yana wannan aikin sa-kai, Li ya kware sosai wajen bayyana fina-finan da suka shafi kimiyya da fasaha, gami da wasan Kungfu ga makafi. Li ya ce:

"Mu dauki fim din 'Jurassic Park' a matsayin misali. A matsayina na namiji, na fi mace saukin bayyana wasu abubuwan dake cikin irin wannan fim da muryata, kamar siffanta yaya dabbar dinosaur take, yaya kukansu yake, watakila mata za su ji kunyar bayyana wannan. Har wa yau, na kan yi amfani da yarenmu na birnin Handan, don bayyanawa makafi fina-finai. Alal misali, idan ka tsoratar da ni, na kan maida martani da cewa 'Wayyo Allah', amma a yaren Handan mu kan ce 'Wayyo' ko jan lumfashi kawai, abun da ke kara kusanta mu da makafi."

Tun shekara ta 2009, ya zuwa yanzu, rassa bakwai na kungiyar masu aikin sa-kai ta "Angel Eyes" suna zuwa kowane gari na birnin Handan, don bayyanawa makafi fina-finai kusan sau 570 a kowace shekara, inda makafin suka kulla zumunci da Kong Yuanyuan gami da membobin kungiyarta, har ma zaman rayuwarsu ya canja sosai.

Kong Suzhen, wata makauniya ce mai shekaru 36 a birnin Handan, kuma cutar makanta ta sa ta rasa kwarin-gwiwa ga zaman rayuwa a dogon lokaci, har ta boye a gida ba ta son mu'amala da saurar al'umma. Daga baya wasu abokananta sun kai ta kallon fina-finai a wajen kungiyar Kong Yuanyuan, inda ta sake karfafa mata gwiwar zaman rayuwa, musamman lokacin da take sauraren fim din Ranaku Hudu na Firaminista Zhou Enlai, wanda Kong Yuanyuan ta bayyana. Kong Suzhen ta ce:

"Ina ta kuka lokacin da nake sauraren fim din da madam Kong ta bayyana mana. Domin kara kulawa da fararen-hula, har tsoffin shugabannin kasarmu, su marigayi Mao Zedong, da marigayi Zhou Enlai ba sa cin nama, maimakon haka suna rabawa fararen hula. Amma mu nakasassu muna da isasshen abinci kala kala a kowace rana, don haka bai kamata mu yi korafi game da zaman rayuwarmu ba, wallahi ina jin dadin zaman rayuwata yanzu. Ina so in yi koyi da madam Kong Yuanyuan, don wata rana ni ma na samu damar bayyana fina-finai ga makafin da suke da bukata."

Sakamakon goyon-bayan da madam Kong Yuanyuan da sauran wasu mutane suka ba ta, a watan Agustar bana, Kong Suzhen ta bude wani shagonta na yin tausa, inda ta ce, tana fatan yin amfani da fasahar tausa don taimakawa karin mutane:

"Burina shi ne a tafiyar da wannan shago yadda ya kamata don kara jawo hankalin mutanen da suke da bukata. Mutane su zo shagona don samun tausa, idan suna da wata damuwa, za su yi hira da mu, za mu kwantar da hankalinsu, ta yadda za su ji dadi. Nakasa ba kasawa ba ce, duk da cewa ni makauniya ce, ina son taimakawa saura."

A halin yanzu, madam Kong Yuanyuan da kungiyarta ta "Angel Eyes" suna himmatuwa wajen kafa wata sinima mai bene uku, a birnin Handan don bayyanawa makafi fina-finai, inda kuma za'a ba su horo don su nakalci fasahohi daban-daban. Madam Kong Yuanyuan ta ce:

"A bene na farko, za mu gina wani dakin fim, guda biyu kuma a bene na biyu. Sa'annan a bene na uku, za mu samar da horon fasahohi iri-iri ga makafin da suke da bukata, ciki har da fasahar yin tausa, da gabatar da labarai da sauransu. Har wa yau, kungiyar kula da harkokin mutanen da suke da bukata ta musamman ta kasar Sin, ta gabatar mana da wata hukumar samar da horo, wadda ta daddale yarjejeniya tare da mu, wato idan makafin wurinmu na da bukata, hukumar za ta samar musu da horon fasahohi ba tare da karbar kudi ba."

Tun farkon farawa, Kong Yuanyuan wata mai fafutukar kare muhallin halittu ce a birnin Handan, har kuma ta kai ga zama shugabar kugiyar masu aikin sa-kai ta "Angel Eyes" don bayyana fina-finai ga makafin da suke da bukata, yanzu kuma tana kokarin taimaka musu wajen samun fasahohi don kyautata zaman rayuwa. Kong ta ce, ita da membobin kungiyarta, ba su taba tsayawa ba, kuma ba za su tsaya ba a hanyar taimakawa mutanen da suke da bukata ta musamman, musamman makafi, inda ta ce:

"Babban burin da muke kokarin cimmawa shi ne, taimakawa makafi samun fasahohi, da gudanar da wasu sana'o'i bisa karfin kansu, ta yadda ba za su ji tsoro ba, har ma su iya bada tasu gudummawa ga sauran mutane. Saboda nakasa ba kasawa ba ce."(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China