Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin za ta nace ga alkawarin da ta yiwa duniya na samun bunkasuwa cikin lumana
2019-10-01 15:51:51        cri

Yau Talata an yi gaggarumin bikin murnar cika shekaru 70 da kafuwar jamhuriyar Jama'ar kasar Sin. A jawabin da ya gabatar yayin bikin, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana cewa, Sin ta samu ci gaba mai armashi dake baiwa daukacin kasashen duniya mamaki sosai a cikin wadannan shekaru 70 da suka gabata, sa'an nan, Sin za ta nace ga wasu manufofinta guda biyar don samun bunkasuwa, ta yadda za a biya bukatun jin dadin jama'a a ko da yaushe da yin kokari wajen tabbatar da dunkulewar kasar baki daya da kuma hada kai da sauran kasashe wajen raya kyakkyawar makomar Bil Adama ta bai daya.

Tsarin nacewa ga jagorancin jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin, da tabbatar da matsayi mai muhimmanci na jama'a, da hanyar gurguzu mai sigar musamman na kasar Sin sun kasance abubuwa na zahiri da suka taimakawa bunkasuwar kasar Sin cikin wadannan shekaru 70, kuma ka'idojin tushe da za a bi wajen samun bunkasuwa nan gaba. Ban da wannan kuma, nacewa ga tsarin samun dinkuwar kasa cikin lumana da kasa daya tsarin mulki iri biyu, matakin da ya kasance hanya mafi dacewa wajen samun dunkulewar kasa waje guda. Ba ma kawai Sin na da karfin tabbatar da zaman lafiya da wadata mai dorewa a Hong Kong da Macao ba, har ma za ta yi kokarin ciyar da bunkasuwar dangantakar babban yanki da Taiwan gaba. Ba wanda zai iya hana dinkuwar babban yanki da Taiwan. Kazalika, nacewa ga hanyar samun bunkasuwa cikin lumana shi ne alkawarin da shugaba Xi Jinping ya yiwa daukacin duniya a madadin 'yan jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin da jama'ar kasar baki daya.

Sin dake bin hanyar samun bunkasuwa cikin lumana da hada kai da cin moriya tare za ta samarwa duniya makoma mai haske wajen samun bunkasuwa da zaman lafiya. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China