Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Manufofin Sin na kiwon lafiyar jama'a sun warware kashi 1 cikin 6 na matsalar kiwon lafiyar adadin al'ummar duniya
2019-10-01 21:28:01        cri
A cikin shekaru 70 da suka gabata, Sin ta bullo da tsarin ba da jinya da kiwon lafiya mafi girma a duniya, wanda ya shafi mutane fiye da biliyan 1 da miliyan 300, yawan mutanen da suka samu inshorar kiwon lafiya ya kai kashi 95 cikin dari bisa na al'ummar kasar Sin. Kwatancin tsawon rayuwar jama'ar kasar Sin a kaddarance ya karu daga 35 zuwa 77. Hakan na nuna cewa, akwai yiwuwar daukacin jama'ar kasar Sin za su samu tabbaci a fannin kiwon lafiya.

Manufar gwamnatin kasar Sin a fannin kiwon lafiyar jama'a, ita ce take nuna karfin al'umma da wadatar kasa, yayin da ake aiwatar da manufofin kiwon lafiyar jama'a, ya kamata a maida hankali ga magance cututtuka, da martaba dokokin kiwon lafiya, kana a kyautata manufofin kiwon lafiyar jama'a, da yin kwaskwarima kan tsarin ba da jinya da kiwon lafiya, da bullo da tsarin kiwon lafiya mai alamar kasar Sin, da tsarin tabbatar da ba da jinya da samar da hidimar likitanci mai inganci, hakan zai taimaka wajen warware kashi 1 cikin 6 na matsalar kiwon lafiyar adadin al'ummar duniya, gami da kyautata zaman rayuwar jama'a. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China