Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Nakasa Ba Kasawa Ba Ce
2019-10-04 14:40:32        cri

Gu Yongqiong mai shekaru 52 da haihuwa, shugabar kungiyar sa kai ta Hengshan ta Yibin dake yammacin Sin ce, kana mai kula da kungiyar kula da yara ta Chunxia. A yayin da take shekaru 3, Gu Yongqiong ta rasa kafarta daya a sakamakon hadarin mota. A lokacin kuruciyarta, malamai da abokan karatu da iyalanta sun kula da ita yadda ya kamata.

"Abokan karatuna sun kula da ni sosai, idan za mu je makaranta, ko muka taso, sun kan taimaka su dauki jakata ta makaranta, a lokacin suna burge ni sosai. Koda yake ba na jin dadi a lokacin, amma sun kula da ni da bani goyon baya, har na samu kwarin gwiwa. A ganina, na samu kulawa sosai, kuma nima ina son kula da mutane." A cewar Gu Yongqiong.

Bayan ta gama karatu, sai ta fara aiki a wani kamfanin gyara motoci dake karkashin kungiyar nakasassu ta lardin Sichuan. Tsohon shugaban kamfanin ya taimakawa mata sosai, tana mai imanin cewa, nan gaba, za ta taimakawa masu bukata. A sakamakon haka, a shekarar 1989, Gu Yongqiong da iyalanta sun koma Yibin inda suka kafa kamfanin gyara motoci na Jingxin.

A shekarar 2014, an kafa kungiyar sa kai ta Chunxia mai kula da yaran da iyayensu suke aiki a waje. Bayan kafa ta, Gu Yongqiong ta shiga kungiyar, yanzu haka tana kula da yara fiye da 40. Ta kan duba wadannan yara a kowane wata, tana dafa abinci su kuma ci tare da su. Ban da samar da kayayyakin taimako, tana kuma kula da halin da suke ciki tamkar mahaifiyarsu.

He Yuxin daya daga cikin yaran da Gu Yongqiong ta taimaka, wadda ke zaune a garin Juexi, gari ne dake kan duwatsu a karkarar birnin Yibin. A sakamakon rashin kyawawan hanyoyin motoci a yankin, abun ne mai wuya a shiga garin ta motoci. Gu Yongqiong ta warware matsalarta ta yin tafiya da kafa daya, ta hanyar amfani da sanda biyu a yankin, ba tare da yin la'akari da yanayin ruwan sama ko iska ba, ta na ci gaba da ziyartar yaran dake zauna a yankin. A ganinta, yaran sun fi bukatar taimakonta. Koda yake da farko wasu yara suna yin watsi da taimakon Gu Yongqiong, amma kasancewar suna ganin yadda Gu Yongqiong ke nacewa ziyarar duk da cewa ta yi tafiya da kafa daya da taimakon sanda guda biyu, tana kula da su kamar mahaifiyarsu,  

"Malama Gu ta kan duba mu sau daya ko biyu a kowane wata, a ganina malama Gu tana da kirki sosai. Malama Gu ta saya mana tufaffi, ta koya mana rawa, ta kula da mu kamar mahaifiyarmu." A cewar He Yuxin.

Chen Wenzhu, 'yar Gu Yongqiong, ta ce a yayin da ta da dan uwanta suke yara , mahaifiyarsu ta kan fita waje ta taimakawa wasu. A lokacin ba su fahimce ta ba, domin ba ta zama tare da su kamar sauran iyaye mata ke zama da 'yayansu. Kana mahaifiyarsu tana fama da nakasa, ta kan yi aikin sa kai har zuwa dare, hankalinsu ba ya kwantawa. Daga baya, mahaifiyarsu ta saka ta da dan uwanta a kungiyar sa kai. Sun fara fahimtar yadda ta ke gudanar da ayyukan sa kai sannu a hankali. Chen Wenzhu ta ce,  

"Yayin da na ga yara sun gama karatunsu, rayuwarsu ta canja, na fahimci cewa, mahaifiyata ta yi aiki mai kyau. Na fara fahimtar yadda ta ke gudanar da ayyukan sa kai sannu a hankali."  

Kafin a kafa kungiyar sa kai ta Hengshan, Gu Yongqiong tana tura ma'aikatanta, ta kuma yi amfani da kudin kamfaninta don gudanar da ayyukan sa kai. Duk da cewa mutane bas a taimakawa Gu Yongqiong da kudi ko kayayyaki, ta taimakawa yara 380 sun kama karatunsu.

A watan Mayu na shekarar 2018, Gu Yongqiong da wasu masu aikin sa kai sun kafa kungiyar sa kai ta Hengshan. Bayan wasu watanni, mutane 248 sun yi rajistar shiga kungiyar sa kai ta Hengshan, mutane kimanin dubu 3 daga bangarori daban daban sun taimakawa kungiyar. Sakataren kula da harkokin jam'iyyar kwaminis ta Sin na kungiyar Hengshan Zhang Chuanke ya bayyana cewa,  

"Dukkanmu mun taru a nan domin tunanin Gu Yongqiong ya burge mu sosai, ta gudanar da ayyukan sa kai ba tare da neman samun suna ba, bayan mun san ta, sai muka fara son yin irin wannan aiki tare da ita."

Bayan kafa kungiyar Hengshan, Gu Yongqiong da sauran membobin kungiyar sun taimakawa yara fiye da 60, wadanda iyayensu suka mutu ko daya daga mahaifansu ya mutu. Yaranta, da ma'aikatan kamfaninta, yaran da ta taimakawa dukkaninsu sun shiga aikin sa kai kamar ta. An samu karin kauna, duk sun kewaye Gu Yongqiong, kana kowa ya san labarinta.

Ma'aikatacin kamfanin Gu Yongqiong Li Jun ya bayyana cewa,

"Na yi farin ciki kamar na samu nasarori da dama domin na taimakawa mutane da dama da kuma sa kaimi ga sauran mutane su shiga kungiyarmu don ci gaba da taimakawa mutane. A karkashin jagorancinta, na gudanar da ayyukan sa kai har na tsawon shekaru fiye da 10, dukkanmu muna goyon bayanta."

A ganin Gu Yongqiong, farin cikin da take samu daga taimakawa mutane ya fi na harkokin cinikayya da sauransu, tana fatan dukkan mutanen da ta taimakawa za su ci gaba da taimakawa wasu a nan gaba. Ta ce,

"Na yi farin ciki, yayin da na ga mutanen da na taimakawa sun fara kaunata, hakan ya fi na harkokin cinikayya ne. Muna kaunar juna, na kan gayawa yara cewa, idan sun girma, sun samu madogara, ina fatan su ma su taimakawa wasu a nan gaba. Wannan ya karfafa min gwiwar ci gaba da gudanar da ayyukan sa kai."

Waka: "Ina godiya domin kin kawo kauna, kin kwantar min da hankali. Kina da sahihiyar zuciya, duk da kuncin da ake fuskanta, amma kin ci gaba da taimakawa wasuˇK" (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China