Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Manufar yaki da talaucin kasar Sin ta samar da dabarun kawar da talauci ga sauran kasashen duniya
2019-10-04 14:44:18        cri

Yau Jumma'a 4 ga wata, gidan rediyon kasar Sin wato CRI ya gabatar da wani sharhi mai taken "Manufar yaki da talaucin da kasar Sin take aiwatarwa ta samar da dabarun kawar da talauci ga sauran kasashen duniya", inda aka yi nuni da cewa, yayin da ake murnar cika shekaru 70 da kafuwar sabuwar kasar Sin, an bai wa masanin kimiyyar aikin noma mai shekaru 90 da haihuwa, wanda ya kyautata ingancin shimkafa lambar yabo ta janhuriyar jama'ar kasar Sin. A kasar Sin, ana samar da isasshen abinci ga al'ummun kasar wadanda adadinsu ya kai kaso 20 bisa dari na daukacin al'ummomin kasashen duniya ta hanyar shukka hatsi a gonaki masu fadin kaso 9 bisa dari na daukacin gonakin fadin duniya kawai, inda adadin hatsin da kasar Sin take samarwa ya kai matsayin koli a duniya a cikin 'yan shekarun da suka gabata, kana a cikin shekaru 70 da suka wuce, gaba daya adadin al'ummun kasar wadanda aka kubutar da su daga kangin talauci ya kai sama da miliyan 850, bisa shirin da aka tsara, kasar Sin za ta cimma burin kawar da talauci a fadin kasar nan da shekara mai zuwa wato shekarar 2020.

Sharhin ya bayyana cewa, a matsayinta na kasa mai tasowa mafi girma a duniya, sakamakon da ta samu a bangaren yaki da talauci a cikin shekaru 70 da suka gabata ya ingiza yunkurin yaki da talauci a fadin duniya, ba ma kawai kasar Sin ta cimma burin yaki da talauci na MDD kafin sauran kasashen duniya ba, har ma ta yi iyakacin kokarin samar da taimako ga sauran kasashen nahiyoyin Asiya da Afirka ba tare da gindayya sharadin siyasa ko wani abu ba, a bayyane ana iya lura cewa, fasahohin da kasar Sin ta samu a bangaren yaki da talauci sun samarwa sauran kasashen duniya baki daya dabarun kasar Sin.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China