Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ni da kasar Sin(3)
2019-10-08 16:29:31        cri

Jama'a masu sauraro, a ranar Talata 1 ga wata ne jamhuriyar jama'ar kasar Sin ta cika shekaru 70 da kafuwa. A cikin shekarun 70 da suka gabata, akwai baki masu dimbin yawa da suka kulla alaka ta musamman da kasar Sin a yayin da kasashensu ke ta kara hulda da kasar ta Sin, ciki kuwa har da baki da suka zo daga kasashen Afirka.

Misali, idan ba a manta ba, a shirye-shiryenmu na baya, mun karanto muku wasu sakwannin da masu sauraronmu suka turo mana wadanda suka nuna sha'awar shiga gasar rubutu da muka shirya mai taken "Ni da kasar Sin", wadanda suka bayyana mana labaransu da suka shafi kasar Sin. To, a wannan mako, mun tsara wani shiri na musamman wanda shi ma ke da taken "ni da kasar Sin", inda za mu gutsura muku labaran wasu 'yan Nijeriya da suke rayuwa ko suka taba zama a nan kasar Sin.

A biyo mu cikin shirin, don jin karin haske.(Lubabatu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China