Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Naomi Osaka tayi nasarar lashe gasar China Open
2019-10-10 18:46:36        cri

Yar wasa Naomi Osaka 'yar kasar Japan da wacce tazo ta biyu Ashleigh Barty sun yi tsokaci game da karawarsu ta karshe da aka fafata inda Osaka ta farfado daga maki 3-6, zuwa 6-3, da kuma 6-2.

Da take jawabi a yayin taron 'yan jaridu bayan kammala gasar, Osaka tace tunaninta ya sauya bayan bude gasar.

"A zagayen farko, maganar gaskiya, abinda kawai nake tunani shine ta yaya zan samu galaba a wasan. Wannan shine abinda ya kara mini kaimi. Ina tunanin wannann bayyanannen al'amari ne. A zagaye na biyu, nayi kokarin tabbatar da komai. Daga nan a zagaye na uku, kawai na ci gaba ne da abinda na faro tun a zagaye na biyu," inji Osaka.

Osaka tace yin gwagwarmaya da irin bugun wasan da Barty take yi al'amari ne mai wahalar gaske kuma hakan ya shafi yanayin wasanta, amma duk da hakan tayi ta kokarin kwatar kanta a zagaye na biyu dana uku.

"Eh, Ina nufin, bayan na gama yin kuka...[bayan gama zagayen farko], mai cike da yawan kura-kurai wajen samun maki, amma duk da hakan na samu maki. Kawai sai na fadawa kaina cewa idan na dena daukar lamarin da wasa zan iya yin nasara. Ina tunanin wannan shine abinda na yi a zagaye na biyu da na uku.

Maganar gaskiya ban taba tsammanin zan yi wani abin azo a gani ba lokacin da tayi mini zarra. Kawai dai nayi ta kokarin samun galaba akanta ne. Eh, ina jin tamkar ina buga wasa a matsayin wacce tazo ta biyu ne a yau, inji Osaka.

Barty, a nata bangaren, tana alfahari da irin kwazon data nuna.

"Ina tunanin wasan yayi kyau. Wasan yana da matukar inganci. Ina tunanin akwai wasu lokuta dana yi abubuwan da suka dace, kuma na kaddamar da abubuwan da suka dace. Ba al'amari bane mai sauki buga wasa da irin wannan kwararriyar. Abu ne mai wahala yin galaba akan Naomi. Abinda kawai za'a yi la'akari dashi shine, wannan muhimmin kokari ne da aka fafata kansa a cikin dare," inji Barty.

Sannan kuma ta yabawa abokiyar karawarta bisa kokarin data nuna wajen tsayawa tsayin daka kuma tayi amfani da damarta domin samun galaba a wasan.

Dominic Thiem wanda ya samu matsayin farko a gasar China Open bayan da ya fardado a wasansa na zagayen farko daga ci 3-6, zuwa 6-4, da kuma 6-1 wanda yayi galaba kan Stefanos Tsitsipas mai matsayi na uku a gasar.

Thiem wanda yayi karin haske game da rawar da ya taka a fagen wasannin a lokacin taron manema labarai bayan kammala gasar.

Yace,"Wannan rana ta yau ta kasance daya daga cikin ranaku mafiya muhimmanci a rayuwata. Irin salon wasan da na buga da kuma matsayin da na samu, babu shakka wannan shine daya daga cikin manyan nasarori da na cimma a rayuwata saboda wasan yana da tsanani sosai, yin kunnen doki a wasan yana da wahala sosai. Lamarin ya sanya ni farin ciki matuka kasancewar na zamo zakara a wasan na karshen mako," inji Thiem.

Thiem, wanda ya kammala zagaye na hudu na wasansa na shekara wanda yayi nasara a gasar Beijing ranar Lahadi, ya bayyana cewa Tsitsipas abokin karawa ne mai kwazo, musamman irin yadda yake kare kansa.

"Ya buga wasa mai ban mamaki a zagayen farko. Na sha wahala matuka a fafatawar. A koda yaushe idan nayi yunkurin mayar da kwallon da ya buga mini, bana samun nasarar data dace. Ya kawo mini hari kai tsaye kuma yana sa kai a hare haren da nake kai masa. Ba don wannan kokarin da yayi ba, da bai kai cimma nasara ba.

Wannan shine dalilin da yasa nayi ta kokari a hare haren da ya dinga kawo mini domin na baiwa kaina karin lokaci, ba don na tsaya tsayin daka wajen kare kaina daga hare haren dan wasa kamarsa ba, da ban kai ga samun nasara ba," a cewar Thiem.

Yayi karin haske game da shirye shiryen da yayi na tunkarar wasan karshe a gasar ta wannan mako da cewar muhimmin al'amari ne.

"Nayi kyakkyawan shiri a wannan wasan. Tun daga farko wasan Laver Cup wanda na fara bugawa. Na shigo gasar da cikakken kwarin gwiwa, na taka muhimmiyar rawa a gasar wasan kwallon tennis tun a wasan farko da na buga. Tabbas, ba lallai bane ka tsammaci zaka iya zama wanda yayi nasara a gasar. Wannan ne dalilin da yasa nake cike da matukar farin ciki saboda nayi nasara, inji shi. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China