Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin ta yi Allah wadai da matakin majalsar wakilan Amurka na amincewa da doka kan HK
2019-10-16 16:54:22        cri
Ofishin kula da harkokin HK da Macao na majalisar gudanarwar kasar Sin, ya yi tir da kakkausar kalamai, kan zartar da dokar kare 'yancin bil adama da Demokradiyya ta 2019 ta HK, da majalisar wakilan Amurka ta yi.

Kakakin Ofishin Yang Guang, ya ce yunkurin tsoma baki ne cikin harkokin cikin gidan kasar Sin, wanda ya nuna goyon baya karara ga ayyukan masu tsattsauran ra'ayi da 'yan adawa, tare da bayyana manufofin malisar wakilai da wasu 'yan siyasar Amurka, wadanda ke yunkurin dakile ci gaban kasar Sin ta hanyar fakewa da batun HK. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China