Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi Jinping ya mika sakon murnar gudanarwar taron yanar gizo na masana'antu na shekarar 2019
2019-10-18 13:57:48        cri
Yau Jumma'a, an bude taron kolin yanar gizo na masana'antu na kasa da kasa na shekarar 2019 a birnin Shenyang na lardin Liaoning na kasar Sin. A sakon taya murnar bude taron da ya aike, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ce, a halin yanzu, ana ci gaba da samun bunkasuwar kimiyya da fasaha da harkokin masana'antu cikin sauri, kuma fasahohin yanar gizo na masana'antu suna ci gaba da bunkasa, lamarin da ya baiwa karfi ga kasa da kasakasashen duniya karfin raya tattalin arzikinsu ta sabbin hanyoyi, da kuma samar da damammaki ga bunkasuwar sana'o'i daban daban cikin hadin gwiwa da kasahen duniya baki daya.

Ya kuma kara da cewa, kasar Sin tana mai da hankali matuka kan bunkasuwar aikin yanar gizo na masana'antu, kana tana son yin hadin gwiwa da gamayyar kasa da kasa domin inganta aikin samar da sabbin kayayyaki, da raya harkokin masana'antu da sadarwa cikin hadin gwiwa a dukkan fannoni. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China