Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Tattalin arzikin kasar Sin yana gudana ba tare da wata tangarda ba
2019-10-18 20:14:43        cri

Babban rukunin gidan rediyo da talabijin na kasar Sin CMG ya rubuta wani bayani mai taken "Tattalin arzikin kasar Sin na samun bunkasuwa mai inganci ba tare da wata tangarda ba, kuma ba ya fargabar duk wani kalubale". Alkaluman da hukumar kididdigar kasar Sin ta fitar a yau Juma'a na nuna cewa, GDPn kasar ya karu da kaso 6.2 a cikin farkon watanni uku na bana bisa na makamancin lokaci na bara, karuwa mafi sauri a duniya, abin da ya shaida cewa, tattalin arzikin Sin na bunkasa mai inganci kuma zai iya tinkarar duk wasu kalubaloli.

Bayanin ya kuma nuna cewa, tsarin tattalin arzikin kasar ya ci gaba da kyautata a cikin wadannan watanni da suka gabata, sha'anin samar da hidimma ya ba da jagoranci matuka wajen raya tattalin arzikin al'umma, kana an samu bulla sabbin sana'o'i da tsare-tsare da kuma nau'o'in kasuwanci, yawan kudin da aka kashe a fannin sayan kayayyaki ya ba da gudunmawa ga karuwar GDP da kaso 60.5 cikin dari, matakin da ya bayyana cewa, tsarin kyautata zaman rayuwar jama'a da gwamnatin Sin take dauka na taimakawa sosai wajen gaggauta bunkasuwar tattalin arzikinta.

Kazalika, bayanin ya nuna cewa, dalilin da ya sa Sin ke da karfin tinkarar koma bayan matsin lambar tattalin arizki ya kasu kashi uku, na farko, aiwatar da managartan manufofin kudi da manufar daidaita darajar kudi da Sin take dauka; na biyu, kara karfin bude kofa ga ketare don kara saurin zamanintar da tsarin tattalin arziki; na uku, kamfanonin kasar Sin na sauke nauyin dake wuyansu wajen karfafa kirkie-kirkiren da ya dace don gaggauta bunkasuwar tattalin arzikin kasar. Ko shakka babu, Sin za ta zama jagorar bunkasuwar tattalin arzikin duniya, saboda yadda take sahun gaba wajen samun bunkasuwar tattalin arzikin tsakanin manyan kasashen duniya da yadda take kyautata tsarinta, matakin da zai ci gaba da zama mai muhimmanci ga ci gaban tattalin arzikin duniya. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China