Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasashen yamma suna daukar ma'auni iri biyu kan tashe-tashen hankula da aka samu a Hong Kong da Catalonia
2019-10-20 17:03:37        cri

Yankin Catalonia mai cin gashin kai na kasar Spaniya a watan Oktoban shekarar 2017 bai yi la'akari da hukuncin da kotun tsarin mulkin kasar ta yanke ba, har ya jefa kuri'ar raba gardama kan tsarin siyasa na neman "'yancin kai". A karshen watan Oktoban shekarar, gwamnatin kasar ta sake karbar mulkin gashin kan yankin. A ranar 14 ga watan Oktoban shekarar da muke ciki, kotun kolin kasar Spaniya ta yanke hukuncin daure tsohon mataimakin shugaban yankin Catalonia Oriol Junqueras da sauran tsoffin manyan jami'an yankin masu zaman kansu wadanda yawansu ya kai 9 a gidan kurkuku. Daga nan, sai aka dinga samun zarge zarge da tashe-tashen hankula a birnin Barcelona. Masu zanga-zangar nuna karfin tuwo sun lalata na'urorin jama'a, da kai farmaki kan yan sanda, sun jefa birnin cikin yanayin tashin hankali, bangaren yan sanda ma sun yi ta sintiri da motoci masu sulke don kwantar da hankali. Ba kamar yadda suka bayyana goyon bayan masu zanga-zanga na Hong Kong ba, a wannan karo, wasu gwamnatoci, kungiyoyin kasa da kasa da kafofin watsa labaru na kasashen yamma da dama, ciki har da Turai da Amurka sun yi shiru sakamakon la'akari da moriyar kansu, ba shakka an gano ma'auni iri biyu ne suka dauka kan irin wannan lamarin.

 

Game da ra'ayin kafar yada labaran BBC, dan majalisar dokokin Scotland Gavin Newlands ya bayar da labari a dandalin sada zumunci a safiyar ranar 17 ga wata cewa, "yanzu dai karfe 7 da minti 7 ne, amma BBC bata bayar da duk wani labari game da yadda Catalonia take a daren jiya ba, a maimakon haka, ta bayar da wani sabon labari game da majalisar dokokin Hong Kong."

A nasa bangaren, wani masanin kasar Indiya Madhav Das Nalapat ya bada sharhi a ranar 18 ga watan Oktoba a jaridar Pakistan Observer, inda ya ce, yankin Catalonia ba zai manta da yin shirun da tarayyar Turai (EU) ta yi ba. Ya ce, EU na mayar da ita a matsayin wadda ke goyon bayan 'yancin kai da gashin kai, kuma ta kan nuna fim na jan hankali ga sauran kasashe. Amma, ba koda yaushe ta yi haka ba, ga misali, ta kan yi fatali da matsalar hakkin bil Adama da kasashe mambobin kungiyar NATO suka tayar a wasu kasashe, ciki har da Libya, Syria da dai sauransu. (Mai fassara: Bilkisu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China