Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
IMF ya yi alkawarin tallafawa Somaliya wajen samun sassaucin nauyin bashi
2019-10-21 10:31:22        cri
Asusun bada lamini na kasa da kasa (IMF) ya bayyana aniyarsa na tallafawa kasar Somalia a yunkurin kasar na neman sassauci daga nauyin basukan dake wuyanta ta hanyar wani shirin saukakawa kasashe matalauta.

Kristalina Georgieva, manajar daraktar IMF, wacce ta tattauna da firaministan Somali Hassan Ali Khaire, ta yi alkwarin yin aiki tare da wakilan mambobin asusun domin samar musu da kudaden da za'a yi amfani da su wajen warware dunbun basukan dake wuyan kasar.

Georgieva ta fada cikin wata sanarwar da aka fitar bayan kammala tattaunawar da yammacin ranar Asabar cewa, tabbatar da nuna hazakar yin aiki tukuru tare da tallafin abokan hulda na kasa da kasa, zai sharewa kasar Somali hanya wajen samun damar rage nauyin bashin dake wuyan kasar a nan gaba.

A cewar hukumar ta IMF, ana bin kasar Somalia bashin kasashen waje kimanin dala biliyan 5, amma Mogadishu ba ta gudanar da wani aiki ko kuma yunkurin biyan basukan ba tun bayan da kasar ta tsunduma yakin basasa shekaru 20 da suka gabata, matakin da ya hana kasar samun damar karbar bashi daga asusun na IMF. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China