Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin ta zo na biyu a fannin ci gaban intanet a duniya
2019-10-21 11:22:42        cri

Kasar Sin ta zo na biyu a fannin raya harkokin intanet a duniya, inda take bin bayan Amurka.

Rahoton raya harkokin intanet na bana da aka fitar a jiya, ya ce kasar Sin ce kan gaba cikin kasashen duniya a fannin amfani da intanet, sannan ita ce ta biyu a fannin karfin kirkire-kirkire da raya sana'o'i.

Rahoton wanda aka fitar a wajen taro karo na 6 kan harkokin intanet a duniya da aka yi a garin Wuzhen na lardin Zhejiang dake gabashin kasar Sin, ya ce kasar na da damar inganta ci gaban kayayyakin intanet da karfin tsaron intanet.

A cewar wani rahoton na daban da aka fitar a jiya, kan ci gaban intanet a kasar Sin, a shekarar 2018, yawan tattalin arzikin kasar Sin a fannin intanet ya kai yuan triliyan 31.3, kwatankwacin dala triliyan 4.4, wanda ya mamaye kaso 34.8 na alkaluman GDP na kasar. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China