Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi Jinping ya bukaci a zurfafa mu'amala da tsibirran kasashen yankin Pacific
2019-10-21 11:30:21        cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aike da wasikar taya murna ga taron dandalin hadin gwiwar raya tattalin arzikin Sin da tsibirran kasashen yankin Pacific karo na uku wanda aka bude a yau Litinin a Apia, babban birnin Samoa.

A wasikar da ya aike, Xi ya bayyana cewa, taron shugabannin tsibirran kasashen yankin Pacific wanda aka gudanar a Papua New Guinea a watan Nuwambar shekarar 2018, ya yi sanadiyyar cimma matsaya wajen daga matsayin dangantaka tsakanin Sin da tsibirran kasashen yankin Pacific zuwa muhimmin matsayin dangantakar mutunta juna da neman cigaba tare.

Xi ya nanata cewa, shirya taron dandalin hadin gwiwar raya tattalin arzikin Sin da tsibirran kasashen yankin Pacific, wata muhimmiyar matsaya ce da aka cimma da shugabannin tsibirran kasashen yankin Pacific. Yana fatan bangarorin biyu za su zurfafa tattaunawa, da tuntubar juna, da yin cudanya ta hanyar wannan dandali, domin samun nasarar bunkasuwa tare. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China